Ƴan ci rani sun shiga mawuyacin hali a Lebanon

Spread the love

Hukumar Kula da ƙaurar Baƙi ta Majalisar ɗinkin Duniya IOM ta ce dubban ‘yan ci rani da ke aiki a Lebanon na cikin tashin hankali, biyo bayan tserewar da Iyayen-Gidansu ke yi ba tare da su ba, domin gujewa hare-haren Isra’ila a sassan ƙasar ta Lebanon.

Cikin rahoton da ta fitar IOM ta ce daga cikin baƙin da ke ganin takansu har da waɗanda ke kulle a gidajen da suke aiki babu damar fita, bayan tserewar da aka yi ba tare da su ba.

Shugaban ofishin hukumar ta IOM da ke Lebanon Mathieu Luciano, baƙi ‘yan ci rani daga ƙasashen Habasha da Kenya, da Sri Lanka, da Sudan, Bangladesh da kuma Phiippines kimanin 170,000 ne akasarinsu mata ke aiki a Lebanon, da dama daga cikinsu kuma sun rasa tudun dafawa, abinda ya sanya su fakewar wucin gadi a wuraren da suka rakuɓe, yayin da wasu kuma ke kulle a cikin gidajen da suke,, bayan da masu gidansu suka cika rigunansu da iska don gujewa hare-haren Isra’ila da ke hanƙoron murƙushe mayaƙan Hezbollah.

Babban jami’in na IOM ya ƙara da cewar babban ƙalubalen da suke fuskanta a yanzu haka shi ne rashin kuɗaɗen biyan buƙatun ɗimbin baƙin da ke neman agajin kwashe su zuwa ƙasashen su, waɗanda ya ce yawansu ƙaruwa yake a kullum.

Ya zuwa yanzu mutane fiye da 2,000 Isra’ila ta kashe a Lebanon, tun bayan hare-haren da ta ƙaddamar daga rabar 23 na Satumban da ya gabata, a yankunan Kudanci da kuma sassan Beirut babban birnin ƙasar. RFI

By ukarofi