Rigima ta sake kaurewa a PDP, an dakatar da Damagum da sakataren jami’yyar

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Rikicin da ake samu a cikin PDP ya nuna babu alamar samun sulhu bayan da wani ɓangare na kwamitin gudanarwar jam’iyyar (NWC) ya dakatar da shugaban jam’iyyar na ƙasa, Umar Damagum da Sakatare na ƙasa Samuel Anyanwu kan zargin su da zagon-ƙasa wa jami’yyar.

Da farko dai, wani ɓangare na NWC ya haɗe-kai da Damagum ne inda ya sanar da dakatar da mai bai wa jami’yyar shawara kan hakar shari’a, Kamaldeen Ajibade da Sakataren yaɗa labara, Dabo Olugunagba, su ma kan zargin zagon-ƙasa.

Saidai, cikin wata takarda da Olugunagba ya fitar a ranar Juma’a, shi ma ya sanar da dakatar da Damagum da Anyanwu.

Ya ce, sun dakatar da su daga shiga harkokin da suka shafi duk zama da jami’yyar za ta yi da sauran shirye-shirye da ta ke gudanarwa har zuwa lokacin da kwamitin ladabdtarwa zai kammala bincike game da su.

By Babaji