Gwamna Abba ya bada tallafin N100m ga waɗanda gobarar kasuwar Kantin Kwari ta shafa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf a madadin gwamnatin jihar ya sanar da bada tallafin Naira miliyan 100 ga waɗanda iftila’in gobara ta rutsa da su a kasuwar Kantin Kwari da ke jihar.

Gwamnan ya faɗi hakan ne a lokacin da ya jagoranci tawagar manyan ma’aikatan gwamnatinsa zuwa kasurwar a yau Juma’a don jajenta musu.

Cikin wata takarda da Kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, Gwamna Abba ya ce gwamnatin jihar na jajenta wa waɗanda shagunansu suka ƙone ya yayin aukuwar lamarin.

Ya ce, tallafin ba ya nufin biyansu asarar da suka yi na iftila’in, sai dai wani ɓangare ne na rage musu raɗaɗin damejin da hakan ya haifar.

Ya kuma tabbatar musu da cewa, gwamnati za ta tabbatar da an samar da muhallin da ya dace don gudanar da harkokin kasuwanci a kasuwar cikin walwala ta hanyar sanya fiitilu masu amfani da hasken rana, gyara hanyoyin da su ke zirga-zirga, gina magudanan ruwa da samar da rijiyoyin burtsatse na zamani.

Gwamna Abba ya yi kira ga hukumar gudanarwa ta kasuwar ta samar da shirye-shirye da za su taimaka wa dubunnan ƙananan ƴan kasuwa wajen yin harkokinsu cikin lumana ba tare da fuskantar tseko ba, ya na mai cewa gwamnatinsa za ta taimaka don ganin Kano ta cigaba da zama cibiyar kasuwanci ta Arewacin Nijeriya da ma wasu ƙasashen Afirka ta Yamma.

Shugaban kwamitin manyan ƴan kasuwa, Alhaji Sabi’u Baƙo ya yi godiya ga gwamnan ganin yadda ya nuna damuwa ga al’amarin tare kira a gare shi ya taimaka wajen warware matsalolin da suka addabi kasuwar.

By Babaji