Haƙiƙanin bayanai game da yaƙin Gaza – Ofishin jakadancin Palestine

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Gidajen jaridu masu ɗaukar ɓangaranci daga yankin Yammacin duniya sun yi ta yaɗa labarai da ke tattare da ƙarairayi, waɗanda ke cike da zarge-zarge marasa tushe ko asali game yaƙin Gaza.

Babbar abin tambayar a nan ita ce, mene ne haƙiƙanin abin da ya faru? Wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun Ambasadan ofishin jakadancin ƙasar Palestine, Abdullah M. Abu Shawesh, ta yi bayani kamar haka;

Dole sai Majalisar Ɗinkin Duniya ta naɗa kwamitin bincike tare da samar da rahoto na ƙarshe da yin adalci kan waɗanda aka tabbatar su na da hannu acikin laifukan yaƙi.

“Mu ƴan ƙasar Palestine, a shirye mu ke mu bai wa duk wani kwamitin bincike haɗin-kai ko yunƙurin samo bayanai na gaskiya ko ma hukumar bincike.”

Takardar ta ƙara da cewa, shekaru 57 kenan da Isara’ila ke yaƙar Palestine ta hanyar kashe al’ummarta da lalata dukiyoyin ƙasar wanda aciki akwai kashe yara ƙanana inda ake ƙone waɗansu da mayar da wasu marayu.

Aƙalla yara 16,927 aka kashe inda aka mayar da wasu 17,000 marayu, yayin da mata 11,487 ne suka rasa rayukansu.

Haka nan, an jefa wasu 60,000 cikin mawuyacin hali saboda rashin ba su kulawa ta lafiya.

Bugu da ƙari, mata 155,000 ne ke fuskantar ƙalubale daban-daban wajen samun kulawa kafin da bayan haihuwa.

Kaso 96 na mutanen Gaza suna fuskantar matsanancin hali na rashin wadataccen abinci wanda ciki har da mata masu ciki 49,300.

Yara 36 ne suka rasa rayukansu saboda matsalar yunwa da rashin ruwan sha mai kyau.

Haka nan, kashi 65 na hanyoyi an tarwatsa shi da kuma rushe gine-gine 31 na jami’o’i yayin da aka lalata wasu ɓangarori na wasu guda 55.

Sakamakon haka ne ɗaliban kwaleji 88,000 da farfesoshi 5,000 suka ɗaiɗaice.

Ma’aikatar harkokin addini ta Palestine ta ruwaito cewa, ma’aikata da masu wa’azi 238 ne aka kashe yayin da aka kama 19 da kuma tarwatsa masallatai 814.

Ƙari akan haka, shine tarwatsa coci guda uku da maƙabartu takwas da sauran ababe da suka lalace sanadiyyar yaƙin.

By Babaji