Daga IBRAHIM MUHAMMAD rahim a Kano
Jami’in riƙo kuma daraktan mulki na ƙaramar Hukumar Fagge, Kwamared Abdullahi Gwarzo ya bayyana cewa kula da harkar tsaro na da mutuƙar muhimmanci a rayuwa “wanda idan babu tsaron ba zaman lafiya idan ba zaman lafiya ba mulki kuma babu al’umma.”
Ya ce don haka ne ma suka bai wa harkar tsaro kulawa dpn haka abinda ya soma shine ganawa da masu ruwa da tsaki kan tsaro na ƙaramar hukumar don samun rahoto na halin da ake ciki a kowane lungu da saƙo da abinda ya kamata a yi hakan tasa suka ɗauki mataki na gaggawa jami’an tsaro da ‘yan sintiri na ƙoƙari wajen aiki ba dare ba rana wajen kula da tsaro.
Ya ƙara da cewa duba da Fagge na da kasuwanni manya da sauran ƙabilu amma Allah a cikin ikonSa ba za ka ji an ce wani abu na matsalar tsaro gagarumi ya faru ba yanzu haka sun tattauna da jami’an tsaro nan gaba ma za su sake zama da su idan da wani abu da ya ɓullo su yi ƙoƙarin toshewa.
Ya ƙara da cewa za su cigaba da tattaunawa da jami’an tsaro hakimi da Dagatai da masu unguwanni su sanar dabsu duk inda aka ji wani abu a sanar da su kuma duk mai unguwa ko dagacin da aka samu bai yi abinda ya kamata ba za a sanarwa ofishin Hakimi a hukunta shi.
Ya ce yanzu sun sa harkar tsaro a abu na farko wanda dole ne sai an samar da zaman lafiya sannan al’umma za ta zauna lafiya sannan a yi mata abinda ya kamata.
Kwamared Abdullahi Muhammad Gwarzo ya ce kasancewar Fagge tamkar wata ƙaramar Nijeriya ce da take ɗauke da ƙabilu daban-daban da ke zaune a cikinta duk lokacinsa za su yi taro akan tsaro ko wani abu suna kiran shugabanninsu su sanar dasu abinda Gwamnati take ciki su sanarwa mutanensu akwai sarakunan Yarbawa da na Ibo dana sauran ƙabilu duk ana zama da su har da shugabanninsu na majami’oi da limamai ana zama dasu a sanar dasu halinsa ake ciki shi ya sa ba a jin wata kururuwa ta matsalar tsaro a yankin Sabongari.
Ya ce ko a kansiloli na riƙo da aka yi a baya daga cikin ƙabilu mazauna Fagge an naɗa wasu daga ciki kuma yanzu duk abinda ake a siyasance da su suke mu’amala don su za su isar da saƙon Gwamnati basu da matsala dasu sun jasu a jiki ana tare ba tare da bambanci ba
Kwamared Abdullahi Muhammad Gwarzo ya ce duba da yanzu ambata fatattakar yan ta’adda daga Zamfara, Sakkwato ana zargin suna gudawa zasu iya tahowa Kano saboda haka sun bada umurni babu wani dagaci ko mai unguwa da zai ga an sauƙi mutum ba tare da ya yi ƙoƙari ya sanar ba.
Yanzu haka jami’an tsaro na farin kaya a yankin sun shaida masa cewa suna da ido sosai a yankin Jaba duk mutumin da ya zo sai an ɗauki bayanansa a tura inda ya fito sannan za a ga yiwuwar a bar shi ko a kore shi.
Kwamared Gwarzo ya ce yanzu haka sun jaddada kwamitin da tsohon kantoman riƙo ya kafa kafin ya tafi na tattara haraji suka sa yana zagayawa lungu da saƙo dan tabbatar da kuɗaɗenda ake tattaunawa suna shigowa asusun ƙaramar hukuma yanzu abubuwa sun sauya ana samun cigaba.
Ya yi kira ga al’ummar Fagge a cigaba da bai wa gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf da mataimakinsa Kwamared Abdussalam Abubakar wanda shine Kwamishinan ƙananan hukumomi goyon baya da za a samu a yi wa al’umma abinda zai amfane su a rayuwarsu yanzu ɗan zuwan gwamnatin Abba tana ƙoƙarin inganta rayuwar al’umma duk da matsatsi da ake ciki.
Ya yi kira ga al’ummar Fagge su cigaba da bai wa ƙaramar hukumar haɗin kai da goyon baya domin su yi shugabancin riƙon lafiya su gama lafiya su kuma bai wa shugabanni da za a zaɓa goyon baya in sun zo su yi wa al’umma abinda ya kamata na cigaba.
