Sojoji sun hallaka ‘yan fashin daji biyu da suka zo ɗaukar kuɗin fansa

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Sojoji sun harbe ‘yan fashin daji guda biyu har lahira a yayin da suka yi yunƙurin karɓar kuɗin fansa na Naira 1.5 na mutane 4 da suka yi garkuwa da su a ƙauyen Mai-Iddo dake ƙaramar hukumar Kachia ta jihar Kaduna.

Daily Trust ta rawaito cewa rahotanni sun bayyana cewa mutanen da aka yi garkuwa da su sun haɗa maza 3 da ƙaramin yaro ɗaya da aka sace su makon da ya gabata.

Wani shugaban al’umma a yankin ya tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar Daily Trust.

Ya ce, an kashe ‘yan fashin dajin ne a yayin da shugabansu ya umarce su da su je wani wuri, inda aka tsara ajiye kuɗin fansar tare da sakin mutanen da suka yi garkuwa da su.

Ya ce, “An kammala shiri da sojoji da mutumin da zai kai kuɗin fansar. A yayin da ya isa wurin da aka tsara sai sojoji suka yi abinda ya dace.

“A yayin da ‘yan fashin daji biyu suka fito ɗaukar kuɗin fansar, sai sojoji suka buɗe musu wuta inda suka kashe biyu daga cikin su nan take.”

Ya ce sojoji sun ceto mutanen da aka sace tare da miƙa su ga iyalansu.

By ukarofi