Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Wani mai suna Markus Dali mazaunin Sina Kwande a ƙaramar hukumar Michika a jihar Adamawa ya rasa ransa yayin da ya ke ƙoƙarin rabon faɗa tsakanin wasu mutane biyu.
Lamarin ya faru ne a ranar 30 ga watan Agusta lokacin da Dali ya shiga tsakanin Barka Yama da Aleɗ Z. Tari domin ya raba su faɗa.
Daily Trust ta tattaro cewa Barka ya kawo naushi sai ya samu Dali wanda hakan ya sa ya faɗi sumamme, inda daga baya aka tabbatar da mutuwarsa a asibiti.
An kama wanda ake zargin mai shekaru 32, Barka, kuma an tuhume shi da laifin kisan kai a ƙarƙashin sashe na 191 na kundin laifuffuka.
A wata kotun majistare da ke Yola, ɗan sanda mai shigar da ƙara, ASP Francis Audu, ya ba da labarin yadda lamarin ya faru, inda ya bayyana cewa Dali ya yi ƙoƙarin raba masu faɗan biyu amma Barka ya yi masa mugun rauni.
Alƙalin kotun, Majistare Muhammed Njidda ya bayar da umarnin tsare Barka a gidan gyaran hali, har zuwa lokacin da ake jiran shawarar shari’a daga ma’aikatar karɓar ƙararrakin jama’a.
