Farashin gas ya ƙaru zuwa Naira 1500 kan kowane kilogiram

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Farashin iskar gas wanda kowa ke amfani da shi wajen dafa abinci ya ƙaru zuwa Naira 1,500 a kowane kilogiram a daidai lokacin da ‘yan Nijeriya ke kokawa kan tsadar man fetur.

Wannan tashin gwauron zabi ya ƙara farashin silinda mai nauyin kilogiram 12.5 zuwa N17,000 a Abuja, wanda ya ƙaru da kashi 41.6 cikin ɗari tun watan Yuli, inda farashinsa ya kai kusan N12,000.

A jihohin Ogun da Legas, farashin ‘yan kasuwa ya tashi daga Naira 1,300 zuwa Naira 1,500 kan kowane kilogiram, abin da ke ƙara dagula tattalin arzikin Nijeriya.

Suresh Kumar, Manajan Darakta kuma Babban Darakta na kamfanin mai da uskar gas na NIPCO, ya bayyana damuwarsa game da yadda Nijeriya ta dogara kan iskar gas da ake shigowa da shi.

Ya bayyana cewa, sama da kashi 60 cikin 100 na iskar gas a Nijeriya a halin yanzu ana shigo da shi ne daga ƙasashen waje, wanda ke haifar da tsadar iskar gas ɗin.

Wani bincike da aka gudanar a baya-bayan nan ya tabbatar da cewa, farashin iskar gas a jihohin Ogun da Legas ya kai Naira 1,500 kan kowane kilo, yayin da a Abuja kuma, farashin cika kwatankwacin kilo 12.5 na tukunyar gas ya ƙaru da kashi 41.6 cikin 100, wanda ya kai Naira 17,000 wanda a baya ya ke akan Naira 12,000.

A watan Agusta, ƙaramin Ministan Albarkatun Man Fetur (Gas), Ekperikpe Ekpo, ya sha alwashin magance hauhawar farashin iskar gas, inda ya yi alƙawarin haɗa kai da hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki.

ƙarancin samar da iskar gas na cikin gida na ƙara ta’azzara tsadar kayayyaki, lamarin da ya sa ’yan Nijeriya da dama ke neman hanyar dafa abinci, kamar gawayi.

Kwamishinan Muhalli na Jihar Ogun, Ola Oresanya, ya yi gargaɗin cewa ƙarin farashin gas taɓarɓara hanyoyin dafa abinci.

Duk da mummunan ra’ayi, Kumar ya kasance mai kyakkyawan fata cewa haɓaka kayan aikin matatun gida na iya taimakawa rage farashin.

Ya kuma yi nuni da cewa, ya kamata a bunƙasa samar man fetur tare da matatar dangote da sauran kayayyakin da yanzu haka suke samun ɗanyen mai a cikin gida, tare da saukaka dogaro da shigo da kayayyaki da kuma rage illar da canjin kuɗaɗen waje ke yi kan farashin.

“Akwai fata cewa dogaro kan iskar gas da ake shigo da shi zai ragu, yana tasiri sosai kan farashin gida,” in ji Kumar.

Kumar ya jaddada buƙatar saka hannun jari a ayyukan samar da iskar gas don faɗaɗa ƙarfin iskar gas na Nijeriya. “Kimanin da muka yi na baya-bayan nan ya nuna cewa ababen more rayuwa da ake da su na kasa za su iya daukar har zuwa MT miliyan 5 a duk shekara, tare da shirya mu don samar da karuwar samar da iskar gas na gida,” in ji shi.

Tun lokacin da NIPCO ta shiga kasuwar iskar gas a shekarar 2004, NIPCO ta kashe maƙudan kuɗaɗe wajen samar da iskar gas ɗin girki ga ‘yan Nijeriya.

“Kamfanin mu a Apapa, wanda ya fara a 5,000 MT, yanzu yana da aarfin da ya wuce 20,000 MT,” in ji Kumar, yana mai jaddada ƙudurin NIPCO na inganta samar da makamashi na ƙasa.

By ukarofi