Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Cece-kuce ya biyo bayan kalaman barkwancin Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio na kwanan nan wanda ya buƙaci ’yan Nijeriya su bi duk inda suka ga ana rabon abinci kyauta.
Kalaman nasa dai na zuwa ne a daidai lokacin da ’yan Nijeriya ke kokawa kan hauhawar farashin man fetur da kuma illar da yake yi a kayayyaki.
A kwanakin baya ne dai kamfanin man fetur na ƙasa (NNPCL) ya ƙara farashin man fetur da sama da kashi 15, wanda hakan ya zama karo na biyu cikin ƙasa da wata guda, wanda hakan ya sa ya fice daga shirin bayar da tallafi kuma ya kawo cikas ga harkokin kuɗi.
Ana sayar da man fetur a sama da Naira 1,000 kan kowane lita a wurare daban-daban a faɗin ƙasar nan.
Da yake magana a cikin wani faifan bidiyo yayin da yake jagorantar wani taro a Majalisar ɗinkin Duniya, Shugaban Majalisar Dattawan ya ce, “yanzu komai ya yi wuya, duk inda ku ka ga abinci kyauta, don Allah ku hanzarta ku je ku samu”.
A cikin faifan bidiyon, ana iya jin takwarorinsa na dariya bayan wannan kalaman.
Da yake mayar da martani a shafin ɗ, wani ɗan Nijeriya mai suna @shanwatche, ya ce: “Waɗannan mutanen ba su san halin da ‘yan ƙasa ke ciki ba. Wannan abin baƙin ciki ne. Kun talauta jama’a kuma kun zo kuna neman mayar da su mabarata?”
Wani mai suna @ManOfNumɓers ya ce; “Suna jefa al’umma cikin ƙunci kuma a lokaci guda suna masu ba’a. Kuma ‘yan Nijeriya sun yi shiru.”
@ɗ6Blade ya ce; “Suna cikin walwala yayin da miliyoyin ‘yan Nijeriya ke shan wahala.”
@metsamyoung ya ce: “Kun ga yadda suke farin ciki da dariya ga mutane sama da miliyan 200. Masu mulki da dukkan shugabanninmu suna kallon kowa a matsayin bawa kuma suna yin ba’a ga halin da ake ciki a Nijeriya.”
Wannan dai ba shi ne karon farko da aka ji Akpabio yana irin waɗannan kalamai ba.
