Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Wani mai suna Sani Suleiman, mai takardar karatun digirin digirgir (PhD) a sashin koyon Larabci a Jami’ar Umaru Musa ’Yar’adua da ke Jihar Katsina na ɗaya daga cikin matasa 400 da suka samu horo a kan sarrafa fatu a cibiyar koyon sana’o’i ta Katsina.
Sakataren cibiyar koyon sana’o’i ta Katsina malam Ahmed kurfi ya sanar da haka da yake hira da manema labarai a ɗakin taro na cibiyar.
Ya bayyana cewa gidauniyar jihar Katsina da wata ƙungiyar cigaban al’umma (Noor management serɓice limited) suka ɗauki nauyin horarwa har na kwanaki goma.
Ya ce, wannan shiri zai taimaka wa jihar Katsina da gwamnatin tarayya na ganin matasa suna cin gashin kansu.
Sakataren gidauniyar ya ƙara da cewa, cibiyar ta horas da malaman makaranta 306 akan sanin makaman aikin koyarwa.
Ya bayyana cewa cibiyar na kuma bada horo akan harkar ilimi, kiwon lafiya da harkan abin da ya shafi ba yadda tsaftataccen ruwan sha.
Sai malam Ahmed kurfi ya yi kira ga gwamnatocin tarayya da na jiha da kuma ƙananan hukumomi da su tallafawa waɗannan matasa bayan sun kammala samun horo domin su zauna da ƙafafun su.
Haka kuma ya ƙalubalanci matasa da su yi koyi da Sani Suleiman PHD da kada su dogara da takardar digiri kawai, da su yi ƙoƙari su koyi sana’ar hannu.
