Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Kwamitin shugaban ƙasa kan aiwatar da garambawul a ɓangaren harkokin kiwo ya miƙa rahotonsa na farko ga shugaba Bola Tinubu.
Kwamitin ya miƙa rahotonsa ne ga shugaban ƙasa a fadar Gwamnatin Tarayya da ke Abuja ranar Alhamis.
Yayin da ya ke zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan ganawa da shugaban ƙasar, shugaban kwamitin kuma tsohon shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), Farfesa Attahiru Jega, ya ce kwamitin ya samu damar zaƙulo matakan da gwamnatin Nijeriya za ta bi wajen yin amfani wajen inganta kiwon dabbobi a Najeriya.
Ya bayyana cewa takardar mai shafi 152 da aka miƙa wa shugaba Tinubu ta ba da shawarar matakan da gwamnati za ta iya amfani da su wajen daƙile rikicin manoma da makiyaya a faɗin ƙasar nan.
A cewarsa, matsayin kwamitin ya tsaya a kan cewa ba zai yiwu nan take a dakatar da kiwo a fili ba, domin hakan ya kasance hanyar gargajiya ta makiyaya.
Ya yi nuni da cewa, za a iya cigana da kiwo a fili cikin ƙanƙanin lokaci har sai an samu isasshiyar wayar da kan jama’a da isassun kayayyakin more rayuwa da za su bunƙasa harkokin kiwo.
Kwamitin ya tsara wani shiri na shekaru goma wanda zai jagoranci gwamnati don tabbatar da ingantaccen ci gaba a kowane fanni na kiwo a Nijeriya.
Kwamitin ya kuma ba da shawarar amfani da fasahohin wajen kiwon dabbobi a Nijeriya.
A cewar Farfesa Jega, an bayar da cikakken jagora kan ayyukan sabuwar ma’aikatar kiwo ta tarayya da shugaba Tinubu ya sanar kwanan nan a cikin rahoton.
Ana sa ran za a bayyana rahoton kwamitin nan ba da jimawa domin ƙara wayar da kan jama’a.
A cikin watan Yuli ne Shugaba Tinubu ya ƙaddamar da kwamitin shugaban ƙasa kan aiwatar da sauye-sauyen kiwo domin magance matsalolin da ke kawo cikas ga noma da kuma buɗa sabbin hanyoyin da za su amfanar da manoma da makiyaya a tsarin kiwo.
