Jami’an rundunar ’yan sandan jihar Legas daga reshen Denton a ranar Lahadi sun damƙe wasu gungun nakasassu guda uku da suka ƙware wajen ƙwacen babur mai ƙafa uku a unguwar Okobaba, Ebute-Meta a Legas.
Mutanen ukun da aka bayyana sunayensu da Mande Bello, mai shekaru 30, Samsudeen Usman, mai shekaru 23 da kuma Gazali, wanda ba a san shekarunsa ba, an ce ƙwararru ne wajen ƙwacen babur mai ƙafa uku.
Kakakin rundunar ’yan sandan, SP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da kama mutanen uku ga jaridar Blueprint a ranar Lahadi.
Ya ƙara da cewa, direban babur ɗin ne ya kai rahoton lamarin ga sashin ’yan sanda na Denton.
“A ranar 10 ga Oktoba, 2024 da misalin ƙarfe 3, wani direban babur mai ƙafa uku ya kai ƙarar wasu nakasassu a ofishin ‘yan sanda na Denton.
“Yana tafiya a shataletalen Boson Oyingbo a inda matanen ukun suka yi yunƙurin kwace masa babur ɗin sa.
“Sun roƙe shi da ya sauke su a mahaɗar gadar Third-Mainland Bridge, inda da farko ya ƙi tsayawa saboda bai yarda da su ba.
“Mai ƙarar ya bayyana cewa a lokacin da ya yi yunƙurin ajiye su a mahadar, Mande Bello ya fito da wata waya ta kebul ya shaƙe shi inda direban ya yi kokawa da su da ƙarfi ya tafi da Okobaba tare da wasu mutane biyu Mande Bello da Samsudeen Usman yayin da Gazali ya tsere.
“Bayan samun ƙarar, an kama mutane biyu da ake zargi kuma an rubuta bayanansu,” inji shi.
A halin da ake ciki, binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa mutanen ukun sun kware wajen kwace babura masu ƙafa uku daga hannun wasu jama’a da ba a san ko su waye ba a jihar.
