Kamfanin Ɗangote zai janye ƙarar biliyan N100 da ya shigar akan NNPCL da AA Rano da wasu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Rukunin Kamfanin Ɗangote ya ce zai janye ƙarar Naira biliyan 100 da ya shigar kan Hukumar Kula da Tace Albarkatun Man fetur ta Ƙasa (NMDPRA) na bada lasisin shigo da mai ga Kamfanonin man fetur na NNPCL, Matrix, AA Rano da wasu guda huɗu duk da cewa akwai matatar gida da ke samar da tataccen fetur.

Cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar a daren ranar Litinin, ya ce ƙarar da suka shigar a ranar 6 ga watan Satumba, 2024 ta ƙunshi tsohon batu wanda a yanzu ababen da ke faruwa sun sha ƙarfin ƙarar.

Kakakin kamfanin, Anthony Chiejina ya ce waɗanda aka zayyano a cikin ƙarar sun fara tattaunawar sulhu, inda ya kuma ya ce matatar ba ta da burin cigaba da ƙarar.

Ya ce a farkon shekarar 2025 ne za a tada batun wanda a lokacin ne za su sanar da batun janye ƙarar wa al’umma a kotun.

Kamfanin Ɗangote ya ce NMDPRA ta ƙarya dokar man fetur da ta hana bada lasisin shigo da man fetur Nijeriya ba tare da samun ƙarancin sa ba acikin al’umma daga masu samarwa a ƙasar.

Ya ƙara da cewa, yin hakan da NMDPRA ta yi, barazana ce ga kasuwancin kamfanin wanda ya zuba biliyoyin Daloli don samar da man fetur ga al’ummar Nijeriya.

Haka nan, lamarin ya bada damar ƙin saya daga Matatar Ɗangote daga ƴan kasuwan man fetur a Nijeriya.

By Babaji