Fashewar tankar mai: Mutane 181 sun mutu, 80 na kwance a asibiti, Gwamnan Jigawa ya faɗa wa Tinubu

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya bayyana cewa kimanin mutane 181 ne suka mutu sakamakon fashewar wata tankar mai da ta afku a jihar a makon jiya.

Ya ce yayin da mutane 80 ke kwance a asibitoci, jimillar iyalai 210 ne abin ya rutsa da su a ranar 15 ga Oktoba.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ziyarci Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a ranar Talata.

Wata motar dakon mai daga Kano zuwa Nguru a jihar Yobe, ta fashe a Majia, dake ƙaramar hukumar Taura a jihar Jigawa.

Da yake jawabi ga manema labarai na fadar shugaban ƙasa bayan ya ziyarci Shugaban ƙasa, Gwamna Namadi ya ce gwamnatin jihar ta riga ta kafa wani kwamiti mai ƙarfi a ƙarƙashin wani mataimakin Sufeto Janar mai ritaya DIG domin bankaɗo haƙiƙanin abin da ya faru.

Da aka tambaye shi ko gwamnatin jihar za ta gurfanar da duk wanda aka samu da hannu, gwamnan ya bayyana cewa hakan zai dogara ne da sakamakon rahoton kwamitin.

Da yake bayar da ƙarin haske, Gwamnan ya ce, “A halin da ake ciki a yau shi ne muna da mutane kusan 181 da suka mutu sannan kusan mutum 80 a asibitoci da kuma iyalai kusan 210 da lamarin ya shafa.

“Gwamnatin jihar Jigawa ta ɗauki nauyin biyan duk waɗanda abin ya shafa kuma mun yi wa iyalai da yawa ɗauki don ganin sun ci gaba da rayuwarsu. Haka kuma shugaban ya yi alƙawarin shiga tsakani tare da taimakawa waɗanda abin ya shafa.

“Gwamnatin jihar ta riga ta kafa wani kwamiti mai ƙarfi a ƙarƙashin shugabancin wani DIG mai ritaya domin ya binciki musabbabin abin da ya faru tare da baiwa gwamnati shawara kan abin da za ta yi. Haka kuma shugaban ƙasar ya ba da umarni ga Corp Marshall da ta gaggauta yin bincike kan lamarin tare da samar da mafita ta din-din-din kan wannan matsala a ƙasar.”

Gwamnan ya kuma ce ya zo ganin shugaban ƙasar ne domin yi masa barka da dawowa daga hutun shekara sannan ya kuma yi masa bayani game da mummunan haɗarin da jirgin ruwa ya yi.

“Don haka na ga ya dace in zo in yi wa Shugaban ƙasa bayanin abin da ya faru da kuma abin da muke yi a gwamnati sannan kuma na gode masa da ya aiko da tawaga cikin gaggawa jihar bayan faruwar lamarin.

“Haƙiƙa matakin da shugaban ƙasa ya ɗauka ya yaba wa al’ummar jihar Jigawa kuma ina ganin ya dace na zo mu gode masa kan hakan tare da yi masa bayanin halin da ake ciki, game da inda muke da kuma abin da muke ƙoƙarin yi.

By ukarofi