Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
’Yan sanda sun kama wata mata mai shekeru 54 kan zargin ta da fasaƙwaurin harsashi guda 350 a Jihar Yobe.
Rundunar ’yan sandan jihar na zargin matar ne safarar makamai ba bisa ƙa’ida ba daga garin Buni Yadi zuwa Damaturu.
Kakakin rundunar, DSP Dungus Abdulkarim, ya ce dubun matar ta cika ne a Damaturu bayan samun bayanan sirri a kan ayyukanta.
“An kama wata mota ƙirar Golf 3 kuma bayan bincike an gano harsasai guda 350 samfurin 7.62ɗ39mm a ɓoye a cikin kayan wadda ake zargin.
“A halin yanzu ana yi mata tambayoyi domin gano abokan cin mushenta da kuma manufarsu,” in ji shi.
Dungus ya ruwaito kwamishinan ’yan sanda na Jihar Yobe, Garba Ahmed, yana jaddada aniyarsa ta yaƙi da laifuka tare da kira ga jama’a su ci gaba da ba wa jami’an tsaro haɗin kai.
