Gwamnatin Nasarawa za ta fara tantance ‘yan fanshon jihar

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

A yanzu haka hukuma dake kula da harkokin ‘yan fansho a Jihar Nasarawa wato Nasarawa State Pension Bureau a Turance dake birnin Lafiya babbar fadar jihar ta kammala dukkanin shirye-shirye don fara tantace da biyan sama da ‘yan fansho a jihar 1000 wasu basussukan su bayan gwamnatin jihar ta sake ware kimanin zuzuruntun kuɗi sama da biliyan 1 don raba wa ‘yan fanshon ɗin waɗanda suka cancanta a ba su a rabon kuɗin na bana.

Babban darakta janar na hukumar Alhaji Suleiman Musa Nagogo ne ya sanar da haka a lokacin da yake tattaunaws da manema labarai a ofishinsa dake hukumar ranar Talata na mako da ake ciki.

Ya ce jim kaɗan bayan sakin kuɗin ne sai hukumar nan take kamar yadda ta saba ta kama aikin zaƙulo waɗanda suka dace su amfana daga kuɗin na wannan karo wanda gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Injiniya Abdullahi Sule ke bayarws don rage wa ‘yan fashon ƙuncin rayuwa da suke fuskanta a yanzu da sauran su duk da ba gwamnatin sa ce ‘yan fanshon ke bin basussukan ba.

Darakta janar na hukumar ‘yan fashon Alhaji Suleiman Musa Nagogo ya kuma bayyana cewa tuni ma hukumar ta manna sunayen waɗanda za su amfana a karon nan a hukumar inda ta gayyace su su zo zu duba sunayen nasu sannan waɗanda suka ga sunayensu ɗin an kuma sanar da su ranakun da za su bayyana a hukumar don tantancesu tare da biyan su haƙƙinsu ba tare da ɓata lokaci ba inda ya kuma yaba wa Gwamna Abdullahi Sule dangane da karamcin da gwamnatin nasa ke bai wa ‘yan fanshon rukuni-rukuni inda ya ce tabbas hakan yana ba su damar biyan buƙatun su da na iyalansu a yanzu.

Har ila yau darakta janar ɗin Nagogo ya kuma yi amfani da damar inda ya yi kira na musamman ga waɗanda ba su samu kuɗin a wannan lokaci ko ba su yi haƙuri don ana bi rukuni-rukuni ne da zarar aka gama da na wannan karo gwamnan zai kuma cigaba har a ƙarshe kowa ya samu da yardar Allah kana ya buƙaci waɗanda suka amfana da kuɗin na bana su tabbatar sun yi amfani da kuɗin yadda ya dace don amfanar kansu da na iyalansu.

Idan ba a manta ba a bara ma gwamnatin Injiniya Abdullahi Sule ta ware irin wannan zuzuruntun kuɗi sama da biliyan 1 don biya wasu ‘yan fanshon ɗin a jihar ta Nasarawa wasu basussukan su da suke bi gwamnatotin tsofaffin gwamnonin jihar da suka shuɗe kafin zuwansa wato bayan biyan ‘yan fashon kuɗaɗen su na wata-wata akai-akai kenan tun zuwansa a matsayin gwamnan jihar na yanzu ƙarƙashin jam’iyyar APC.

By ukarofi