Matatar Ɗangote ta fara sayar da mai ga ‘yan kasuwa kai tsaye

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Matatar man Ɗangote ta fara samar da man fetur ga wasu ‘yan kasuwar mai kaitsaye ba tare da neman wani kamfanin man fetur na ƙasa ba.

An tattaro cewa, yayin da ƙarin ‘yan kasuwar man ke ƙara zage damtse wajen siyan kayayyakin kaitsaye daga masana’antar, wasu kuma na shigo da kayayyakin, domin ɗaruruwan miliyoyin litar man fetur da ake shigowa da su ya kamata su shiga gabar ruwan Nijeriya nan da makonni biyu.

Ku tuna cewa jaridar ta ruwaito a ranar Litinin cewa aƙalla jiragen ruwa huɗu ɗauke da man fetur da aka shigo da su sun isa tashar jiragen ruwa da ke kan iyakokin ƙasar tsakanin Juma’a, 18 ga Oktoba, da Lahadi, 20 ga Oktoba.

Rahoton ya bayar da misali da wata takarda da aka samu daga hukumar kula da tashar jiragen ruwa ta Nijeriya, wadda ta nuna cewa kimanin lita miliyan 123.4 na fetur ne aka ajiye a tashoshin ruwa guda biyu domin inganta wadatar mai a faɗin ƙasar.

Wannan ci gaban ya tabbatar da wani rahoto da jaridar nan ta buga a baya, wanda ya bayyana cewa dillalan mai na da niyyar shigo da kayan ne domin ƙara samar da kayan da ake samu daga matatar ɗangote dala biliyan 20.

A halin yanzu, yayin da manyan masu sayar da mai ke shigo da kayan, takwarorinsu sun fara ɗauke da fetur kai tsaye daga kamfanin da ke Lekki.

Wani babban jami’i a matatar ya ce a yanzu an ba ‘yan kasuwa damar tuntuɓar kamfanin domin yin mu’amalar kasuwanci kaitsaye bisa son-saye, mai son sayarwa.

“Yan kasuwa sun riga sun zo matatar don daga man fetur. Suna tashi ne kai tsaye daga matatar, ba ta hannun wani ɓangare na uku ba, ”in ji wani amintaccen jami’in, wanda ya yi magana cikin aminci saboda rashin izinin yin magana a kan lamarin.

Majiyar da ta kasa tantance farashin da ‘yan kasuwar ke daga hajar, ta ce dillalan man ba za su zo ba idan har farashin bai yi musu daɗi ba.

“Mun cimma yarjejeniya da wasu ‘yan kasuwa kuma har yanzu ana ci gaba da samun wasu. Ban san ainihin farashin ba, amma idan farashin bai yi kyau ba, ‘yan kasuwa ba za su zo wurinmu ba,” inji jami’in.

Ya ci gaba da cewa al’amura sun inganta, musamman ganin yadda Gwamnatin Tarayya ta fara samar da ɗanyen mai a wurin.

Wani jami’in cibiyar ya nuna wa wani wakilinmu motocin wasu ‘yan kasuwa na lodin kayayyakin kai tsaye daga kamfanin ba tare da bi ta kamfanin NNPC ba.

“Wasu daga cikin manyan motocin da kuka gani a can yau sun fito ne daga ‘yan kasuwa da ke siyan kayan kai tsaye daga ɗangote, ba tare da neman hanyar zuwa NNPC ba. Don haka an fara siyarwa kai tsaye,” majiyar ta bayyana.

Jami’in ya bayyana cewa, saboda yawan buƙatar man fetur a Nijeriya da sauran ƙasashe, matatar ta mayar da hankali wajen tabbatar da kashi 53 cikin 100 na samar da mai daga ɗanyen mai da take samu.

“Za a iya sake duba wannan a nan gaba idan buƙatar sauran kayayyakin da aka gama sun ƙaru fiye da buƙatar man fetur, amma a yanzu kusan kashi 53 na ɗanyen man da muke amfani da shi ana amfani da shi wajen samar da mai, yayin da sauran kayayyakin ke da sauran kashi,” inji jami’in ya bayyana.

Da aka tambaye shi ko ’yan kasuwa sun fara siyan man fetur daga hannun ɗangote kai tsaye ba tare da neman NNPC ba, ɗaya daga cikin manyan ‘yan kasuwar ƙasar nan ya amsa da cewa.

“Eh, komai yana cikin tsari. An ba da shawarar cewa hakan zai faru nan ba da jimawa ba kuma ciniki ne na yau da kullum,” majiyar ta bayyana.

Sai dai wannan ya saɓa iƙirari da wasu gungun matatar man ta yi na cewa matatar man ba za ta iya siyar da mai ga ‘yan kasuwa ba, sai an kawo ƙarshen yarjejeniyar da ke tsakaninta da NNPC.

By ukarofi