Muna amfana da kyawawan ayyuka daga jagoranmu Rabiu Kwankwaso – Bombay Gama

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Jagoran Kwankwasiyya na mazaɓar Gama a ƙaramar Hukumar Nassarawa, Hon. Muhammad Adamu da aka fi sani da Bombay Gama ya bayyana cewa suna matuƙar murna da alfahari da zagayowar ranar haihuwar jagoransu na Kwankwasiyya na duniya, babban jagoran NNPP Injiniya Dokta Rabiu Musa Kwankwaso bisa cikarsa shekaru 68 da haihuwa.

Ya ce sun gode wa Allah da ya ba su dama suke biyayya ga tsarin tafiyar siyasa ta Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da har yau ɗin nan basa nadama akan hakan saboda ɗorasu da yake yi akan Gwadabe na daidai da aƙida ta kyakkyawar siyasa da take haska fitilar taimakon al’ummar da ake jagoranta su amfana.

 Hon. Bombay Gama ya ce tun da Allah ya ba su dama ta bin jagoranci na Madugun Dakta Rabiu Musa Kwankwaso Kwankwasiyya ba su taɓa yin ɗari-ɗari ko dana sanin abinda yake ɗorasu akai ba, saboda tafiya ce na jagoranci na sadaukarwa akan gaskiya da amana, inji shi.

Ya yi nuni da cewa shi dama bin tsarin kyakkyawan  jagoranci umurni ne na Allah kuma duk abubuwa da ake na alkhairi ne, abin sha’awa shine na yadda ya assasa duk ranar zagayowar haihuwarsa da haihuwarsa yana ƙaddamar da muhimmin abu da zai amfani cigaban al’umma.

Hon. Muhammad Adamu Bombay Gama ya ce wannan shine karo na shida da suke gani suka shaida duk shekara yana assasa wani muhimmin aiki na alkhairi mai gudana da har ya koma ga Ubangiji ladan ba zai gushe ba akwai makaranta da ya samar na koyon jinya da ya yi mata suna da sunan mahaifiyarsa haka ya yi masallaci ya sadaukar  da sunan mahaifinsa ya samar da cibiya ta jaddada ƙur’ani kuma yanzu a wannan karon ya samar da manyan ɗakunan nazari a Jami’ar SKY don haka ba abinda za su ce sai yi masa fatan Allah ya yi riƙo da hannayensa akan abubuwan da  yake na alkhairi.

Bombay ya ce wannan  kyakkyawan darasi ne da suke koya daga jagoran nasu yana nuna musu  yin aiki da al’umma zasu amfana dashi a  kowane lokaci.Suna fata Allah ya cigaba da tsawaita ran Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kuma cika masa burinsa na kyautata cigaban ƙasar nan.

By ukarofi