Kocin Real Madrid Carlo Ancelotti ya ce Vinicius Jr zai lashe kyautar Ballon d’Or ta bana da za a yi a ranar 28 ga wannan watan na Oktoba.
Vinicius ya ci wa Madrid ƙwallo uku a wasan da ta yi a jiya da Borussia Dortmund, wanda aka fara zura musu ƙwallo biyu a minti 45 ɗin farko.
Bayan dawowa hutun rabin lokaci ne Madrid ta farke ta ci ƙwallo 5-2, kuma da tasirin Vinicius.
“Zai lashe kyautar, ba wai don ƙwallayen da ya ci ba a daren jiya, saboda abin da ya yi a bara.
“A bara ya taimaka mana mun lashe Champions Lig, yau kuma ya ci uku rigis hakan shi ma zai taimaka masa ya lashe Ballon d’Or na gaba” inji Ancelotti.
Irin wannan bajintar da ba bakon abu ba ne ga Real Madrid, a baya ta yi irin wannan a Zakarun Turai aƙalla sau uku.
Ga duk wata ƙungiya da ta yi irin wannan farkewa da ƙarawar a minti 45, zai zama abin sanon tarihi a gare ta.
Carlo Ancelotti yanzu ya ci wasa biyu a yi rashin nasara ɗaya a Champions, yanzu suna maki iri ɗaya da Dortmund.
Vinicius ya ci kwallo 26 ya bayar da 11 an ci a kakar da ta gabata.
Ya kuma lashe La Liga da Champions Lig ya kuma lashe Supercup de Espana.
