Daga DAUDA USMAN a Legas
Sabuwar kasuwar unguwar Aladiboye ta ƙaramar Hukumar Ikorodu dake cikin jihar Legas ta fara karɓar baƙuncin ‘yan kasuwa da sauran masu sha’awar gudanar da harkokin kasuwanci a jihar Legas da kewayenta gabaɗaya.
Shugaban kasuwar ta Aladiboye dake shiyyar Elepe sabo Ikorodu a cikin garin Legas Alhaji Mohammed Adamu Shamakin Sarkin Unguwar Aladiboye ɗan asalin jihar Adamawa mazaunin Legas shine ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da Jaridar Blueprint Manhaja a Legas jim kaɗan bayan kammala taron su da waɗansu ƙusoshin kasuwar wanda suka saba yi domin neman shawarwari a junansu ta yadda za a yi kasuwar ta ƙara samun ɗaukaka tare da cigabanta baki ɗaya.
Kusoshin kasuwar sun haɗa da shi kansa shugaban kasuwar ta Aladiboye Alhaji Muhammed Adamu da Alhaji Muhammadu Lawan Fiyafiya Sabo Ikorodu da Jibirin Wazirin Sarkin unguwar Aladiboye da sauran manyan ‘yan kasuwa makamantansu.
Da yake yin tsokaci a wajan taron nasu na ƙusoshin kasuwar shugaban kasuwar ta Aladiboye Alhaji Muhammed Adamu ya ce sakamakon cunkoson jama’a da kasuwannin cikin garin Legas suke fama da shi hakan ta sanya suka ƙirƙiro wannan kasuwa ta Aladiboye a shiyyar Sabo Ikorodu domin rage irin wannan cunkoso.
Ya ce akan haka yake ganin ya kamata ‘yan kasuwa da sauran masu sha’awar yin kasuwanci a jihar Legas da su kawo wa wannan kasuwa ziyarar gani da ido domin kuwa ƙofar kasuwar a buɗe take dangane da wannan al’amari.
Hakazalika ya ce kuma za su yi iyakar ƙoƙarinsu a wajen ƙarfafa tsaro a kasuwar da kewayenta gaba ɗaya.
Shi ma da yake gabatar da jawabinsa dangane da abin da ya shafi kasuwar ta Aladiboye a Legas Alhaji Jibiril Waziri ya jawo hankulan ‘yan kasuwar ne da su cigaba da gudanar da harkokin kasuwancin su na yau da kullum a cikin tsafta tare da tausayawa al’umma a wajen samun rangwamen farashi a kayayyakin da ake sayarwa a kasuwar baki ɗaya.
Sauran jawaban da suka fito daga bakunan ‘yan kasuwa da sauran al’umma waɗanda suka samu yin tsokaci a wajen taron dukkan jawaban su sun kar katane a wajan gamsuwa da samun wannan kasuwa ta aladiboye tare da tab batarwa shuwagaban nin kasuwar cewar za su yi iyakar mai yiwuwa a wajen bai wa jagororin kasuwar haɗin kai da goyon baya tare da kawo cigaban kasuwar bakiɗaya.
