Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
A Nijeriya a yau, inda hauhawar farashin kayayyaki ke ci gaba da tayar da farashin kayayyakin masarufi, al’umma na fuskantar matsi wajen biyan buƙatun yau da kullum, musamman abinci.
Tashin farashin kayan abinci na ingiza mutane da yawa cin abubuwan da za su iya yin illa ga lafiyarsu.
Duba da muhimmancin cin abinci mai gina jiki, a halin yanzu nama na neman fin ƙarfin yawancin ‘yan Nijeriya. Farashin naman kaza, kifi, naman sa ko na rago, da ƙwai ya ninka fiye da ninki biyu a cikin shekarar da ta gabata, wanda ya tilastawa mutane yin nisa da shi.
Bincike ya nuna cewa a halin yanzu kilo na kifi yana kaiwa tsakanin N3,500 zuwa N8,000, ya danganta da nau’insa. Ana sayar da kilo na babbar kaza tsakanin N9,000 zuwa N12,000, yayin da cinyar talo-talo ya kai kusan N8,000 kan kowane kilo. Farashin kiret ɗin ƙwai ya tashi daga N2,000 a bara zuwa tsakanin N5,200 zuwa 6,000 a bana.
Hatta kan sa, wanda a da ake samunsa da sauƙi, yanzu farshinsa ya yi matsanancin tsada, inda a yanzu farashin tsoka ɗaya ya kai N700 wanda a da bai wuce tsakanin N20 zuwa 50 ba.
Dangane da halin ha’ula’in, wasu mutane yanzu suna sayen kawunan kifi – wani yankin jikin kifi da ya kamata a jefar ko a bai wa kare – a matsayin nama don samun arha.
