Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Tsohon shugaban tsagerun Neja-Delta, Mujahid Asari Dokubo, ya ce shugaba Bola Tinubu ya ci amanarsa.
A cikin wani faifan bidiyo da ake ta yaɗawa, Dokubo, wanda ya yi wa shugaban ƙasa yaƙin neman zaɓe, ya ce duk da ya ƙarar da duka kuɗinsa wajen zamowar Tinubu shugaban ƙasa, amma an yi watsi da shi.
Ya sha alwashin ƙulla kawance da Arewa, inda ya ce bayan ya kasadar da ransa saboda Yarbawa, bai samu komai ba.
Ya ce, “Ina neman afuwar iyayenmu, domin ba su yi kuskure wajen ƙulla ƙawance da Arewa ba, kuma a matsayinmu na samari yanzu za mu fara wannan ƙawance.
“Daga yau zan yi aiki na ƙulla ƙawance da Arewa. Shugaba Tinubu ya ci amanata ne bayan na kashe duk kuɗina na kwashe na yi masa yaƙin neman zaɓe. Tinubu da na sani a yanzu ba Tinubun da na sani ba ne a baya. Za mu isar da wannan saƙo cewa ’yan Arewa ne kawai za su iya yin aiki da ’yan ƙabilar Ijaw.
“Ba za mu iya aiki da Yarabawa ba; cin amana ne a gare mu. Mun jefa rayuwarmu cikin kasada ta hanyar zaɓe da yin komai, kuma abin da za a mana kenan?”
Ba a dai san lokacin da Dokubo ya samu saɓani da Tinubu ba amma alamu sun nuna cewa ziyarar da ya kai fadar shugaban ƙasa ta bai wa shugaban ƙasa kunya.
Tsohon ɗan gwagwarmayar ya gana da Tinubu ƙasa da wata guda da shugaban ƙasa ya karɓi ragamar mulki inda ya yi jawabi ga manema labarai a fadar.
