Madakin Gini ya yi bara’a da tafiyar Kwankwasiyya

Spread the love

Daga RABIU SANUSI a Kano

Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙaramar hukumar Dala a Jihar Kano, Hon Aliyu Sani Madakin Gini ya bayyana ficewarsa daga tafiyar Kwankwasiyya da ke biyayya da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.

Idan za a iya tunawa Aliyu Sani Madakin Gini na daga cikin na gaba-gaba a tafiyar Kwankwasiyya da yiwa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso biyayya.

Madakin Gini ya bayyana ficewarsa tasa ne daga tafiyar Kwankwasiyya da yammacin wannan rana ta lahadi a mazaɓar ta Dala da ke Jihar Kano.

“Daga yau ni Aliyu Sani Madaki na bar tafiyar Kwankwasiyya, Saboda Kwankwasiyya yaudara ce, Kwankwasiyya cin amana ce, mai girma gwamnan jihar Kano Alh. Abba Kabir Yusif mutumin kirki ne, ina baka shawara ka tsaya da ƙafarka ka da aje fa ka wani rami da bazan bayyana shi yanzu ba”. Inji Ali Madaki.

Ya ce ya shirya tsaf domin tallafawa duk wanda ya biyo shi, yace kowa zai amfana, ya yi alƙawarin zai share sama da kwana 7 domin ganawa da magoya bayansa.

Madakin Gini ya kuma umarci duk wani wanda ya yarda cewa shi ne jagoransa, ya cire jar hula da jajayen mayafai.

Sai dai ɗan majalisar bai bayyana ficewarsa daga jam’iyyar NNPP ba.

By ukarofi