Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya bayyana cewa Nijeriya ta yi asarar sama da Naira biliyan 300 a lokacin zanga-zangar ƙuncin rayuwa da ta gudana a watan Agusta.
Shettima ya bayyana haka ne a yayin wani taro da aka gudanar domin amsar masu zanga-zangar 114 da aka gurfanar a gaba kotu amma wata babbar kotu ta sallame su.
Mai shari’a, Egwatu Obiora ne ya sallami wannan ƙarar kamar yadda lauyan gwamnatin tarayya ya buƙata.
Mataimakin Shugaban ƙasa, wanda ya wakilci Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya miƙa yaran ga gwamnonin jihohin su, gwamnan Kano da Kaduna.
Shettima ya bayyana cewa bisa halin jin ƙai da shugaban ƙasa ya ke dashi, ya umarci a saki yaran nan baki ɗayan su. Ya umarci yaran da su godewa Shugaban ƙasa kuma su zama ƴan ƙasa nagari da za su ciyar da ƙasar su gaba.
