MRS, Conoil da sauransu sun kashe biliyan N833 wajen shigo da fetur

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Manyan ’yan kasuwar mai a Nijeriya sun ci gajiyar manufofin Gwamnatin Tarayya na baya-bayan nan na kawar da tallafin man fetur. Wannan sauyi ya bai wa ’yan kasuwar damar cin karensu babu babbaka a harkar man fetur.

A cikin watanni tara na farkon shekarar 2024, wasu fitattun ‘yan kasuwar mai su huɗu sun bayar da rahoton samun ɗimbin kuɗaɗen shiga, inda suka samu jimillar kuɗi Naira Tiriliyan 1.3 daga sayar da albarkatun man fetur ga ‘yan Nijeriya.

Kamfanonin man sun haɗa da Total Energies Marketing Nigeria, MRS Oil Nigeria, Eterna Plc, da Conoil Plc.

Duk da maƙudan kuɗaɗen da ake kashewa wajen shigo da mai, kamfanonin mai sun kashe biliyan N833.86 wajen shigo da man fetur a cikin wannan lokaci, wanda hakan ya sa ribar da suka samu kan sayar da mai ta kai biliyan N465.92.

Wannan dai ya zo ne bisa ga bayanan kuɗi na watanni tara na kamfanonin kamar yadda aka jera a kasuwar canji ta Nijeriya.

Kamfanonin sun kuma zayyana hauhawar kuɗaɗen gudanar da aiki, tare da samun ci gaban sama da kashi 100 cikin 100 a duk shekara a cikin ribar da suka samu na tsawon watanni tara, sakamakon cire tallafin.

A watan Mayun 2023, gwamnati mai ci ta sanar da cire tallafin, tare da tayar da farashin man fetur tare da haifar da ƙarin kuɗaɗen shiga da riba ga manyan masu sayar da mai. Farashin man fetur ya tashi daga N200 kan kowace lita tun daga ƙarshen watan Mayun 2023 zuwa sama da N1,060 a kowace lita a watan Nuwamba 2024.

Sanarwar ta nuna cewa kamfanonin huɗu sun samu riba mai yawa bayan harajin bikliyan N45.3, wanda ke nuna ƙaruwar kashi 146 cikin 100 a duk shekara daga biliyan N18.5 da aka fitar a daidai lokacin shekarar 2023.

Taƙaddamar da sakamakon ya nuna cewa kamfanonin sun kashe jimillar Naira biliyan 833.86 wajen shigo da mai daga watan Janairu zuwa Satumbar 2024, wanda ya nuna ƙaruwar kashi 99.4 cikin 100 ko kuma N415.76bn daga biliyan N418.1 a daidai wannan lokacin na shekarar 2023.

Yayin da kuɗaɗen shiga daga sayar da man fetur ya ƙaru da kashi 98.4 ko kuma biliyan N644.57 daga biliyan N655.2 da aka samu a shekarar 2023 zuwa tiriliyan N1.29 a shekarar 2024.

By ukarofi