Matar aure ta tilasta budurwa ta kwanta da mijinta don ta haifa masa ’ya’ya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Wata jami’iyar ‘yan sanda mai bincike (IPO) Sufeto Elizabeth Osikolu, a ranar Litinin, ta shaida wa wata Kotun Laifukan Cin Zarafin Jinsi a Ikeja, yadda wata matar aure, Omolara Alashe, ta tilasta wa wata yarinya ’yar shekara 19 ta kwana da mijinta don ta haifa masa ’ya’ya.

Omolara da mijinta, Ramoni Lateef, suna fuskantar tuhume-tuhume guda uku da suka haɗa da haɗa baki, fyaɗe da kuma lalata da ƙaramar yarinya.

Sai dai waɗanda ake tuhumar sun musanta aikata laifin.

A yayin da wani shaida yake magana da babban lauyan jihar, Babajide Boye, a gaban kotu, ya shaida wa kotun cewa lamarin ya faru ne a wani lokaci a shekarar 2022, a Legas.

Sufeto Osikolu ta shaida wa kotun cewa mahaifiyar yarinyar ta rasu da daɗewa a Ojota, inda ma’auratan suka yi tayin ba ta masauki.

Ta shaida wa kotun cewa wadda abin ya shafa ta ce ma’auratan sun daɗe suna lalata da ita a duk lokacin da ta shafe tana zaune da su.

A cewar shaidar, wadda ake ƙara na farko (Omolara) a wata rana, ana zargin ta tada yarinyar mai shekaru 19 a tsakiyar dare, kuma ta tuɓe ta tsirara yayin da wanda ake ƙara na biyu (Ramoni) ya kwana da ita.

IPO ta shaida wa kotun cewa binciken da ta gudanar ya nuna cewa ma’auratan sun haifi yaro amma ya mutu a wani lokaci a watan Oktoban 2022.

Shaidan ya ce, “Wadda ake ƙara na farko ba ta sake samun ciki ba bayan mutuwar yaron.

“Don haka suka yanke shawarar amfani da wadda abin ya shafa domib haifa masa ‘ya’ya don hana mijin sake yin aure.

“Yarinyar ta ce, wata rana suna cikin ɗaki sai wadda ake ƙara na farko ta fara dukanta, ta tuɓe ta tsirara ta sanya mata yatsu a cikin farjinta.

“Bayan ta lakaɗa wa yarinyar duka, ta jefar da kayanta, ta kwace katin ATM ɗinta, layin MTN da kuma albashin da take karɓa a lokacin don hana ta samun kuɗi.”

Yayin da lauyan gwamnati Lekan Egberongbe ke yi masa tambayoyi, shaidan ya ci gaba da cewa yarinyar ba ƙarya take yi ba.

A cewarta, wadda ake ƙara na farko ta amince da hakan a cikin bayanin nata.

Shaidar ta shaida wa kotun cewa da yarinyar ‘yar shekara 19 ta amince da wannan cin zarafi da aka yi mata, da ba za ta kai rahoto ga Hukumar Yaƙi da Cin Zarafin Jama’a (DSɓA) ba.

“Ba za ta gabatar da kanta don duba lafiyarta a cibiyar Mirabel ba.

“Yarinyar da ake magana ba za ta iya tinkarar mutumin ba saboda matar ta tsorata,” in ji Osikolu.

Mai shari’a Oshodi ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 3 ga watan Fabrairun 2025 domin ci gaba da shari’ar.

By ukarofi