Sufeto Janar ya hana jami’an Amotekun da bijilante shiga zaɓen Ondo

Spread the love

Babban Sufeton ‘Yan Sanda na ƙasa, Kayode Egbetokun, ya ba da umarnin haramta wa Ƙungiyar tsaron Yammacin Nijeriya wato Amotekun da kuma bijilante shiga zaɓen gwamna da za a gudanar a ranar 16 ga watan Nuwamba a jihar Ondo. Kwamishinan hulɗa da jama’a na rundunar, Muyiwa Adejobi, ya fitar da wannan sanarwa a ranar Lahadi tare da tabbatar wa da al’umma tsaron zaɓen.

Babban Sufeton ya ce an shirya tura jami’ai daga sassa na musamman na ‘yan sanda domin tabbatar da tsaro a lokacin zaɓen. An kuma tsara yin sintiri ta sama da jiragen helikwafta na ‘yan sanda tare da tura jiragen ruwa domin kiyaye tsaron yankunan tekuna da kogunan jihar.

A yayin da zaɓen gwamnan jihar Ondo ke gabatowa, Sufeton ‘Yan Sanda ya tabbatar wa al’umma cewa rundunar ‘yan sanda za ta ɗauki duk matakan da suka dace domin tabbatar da tsaro a zaɓen a cikin ƙananan hukumomi 18, mazaɓu 203 da rumfunan zaɓe 3,933 a faɗin jihar. Babban Sufeton ya kuma tabbatar da an shirya aiki da cikakken tsaro a lokacin zaɓen.

Rundunar ta yi alƙawarin cewa za ta tabbatar da bin dokokin zaɓe na shekarar 2022 domin tabbatar da gaskiya da adalci a dukkan matakan gudanar da zaɓen. Tare da haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro na Ƙasa, jami’an ‘yan sanda za su tabbatar ba a samu tangarda ko tashin hankali a lokacin zaɓen.

Babban Sufeton ya kuma ja kunnen ‘yan bangar siyasa da duk wani da ke shirin tada zaune-tsaye cewa za su gamu da hukuncin doka idan har suka aikata wani abu na tashin hankali. Ya kuma sanar da cewa kawai hukumomin tsaro na tarayya ke cikin kwamitin tsaro na zaɓen don haka su ne za su halarci wajen zaɓen, domin kiyaye zaman lafiya.

By ukarofi