Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Hon. Bello Jadda Sharifai mataimakin na musamman ga Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf a kasuwar waya na titin Bairut wanda kuma ɗan takarar shugabancin ƙungiyar ‘yan kasuwar waya na titin Bairut ne ya ce takarar da yake ta amsa kiran da matasa da iyaye ne a kasuwar suka yi masa na ya fito bisa la’akari da gudunmuwa da yake bayarwa ga cigaban sana’ar waya.
Ya ce sama da shekaru 20 suke a cikin harkar saye da sayarwa da gyaran wayar sun san matsalolin harkar da al’fanunta da su aka soma kyankyashe sana’ar tun farkon zuwan waya tun daga bakin ‘Post Office’ da “Farm Centre” da titin Bairut duk ana damawa da su.
Hon. Bello Jadda Sharifai ya ƙara da cewa yana da manufofi na alhairi da yawa akan wannan takara tasa musamman na son su da cigaban kasuwar waya na titin Bairut fiye da yanda take a yanzu.
Ya yi nuni da cewa Kasuwar Waya ta titin Bairut ita ce kasuwa guda ɗaya da ake zuwa daga ƙasashen yammacin Afirka ake sayen wayoyi a cikinta da kuma take da tarin shagunan kamfanonin waya amma duk da wannan matsayi na ta abin takaici babu wani mutum tilo ɗan asalin jihar Kano a kasuwar da sauran kasuwanni na waya dake Kano da yake da “Dealership”.
Ya ce akwai abokan zamansu da ba ‘yan asalin jihar Kano ba, su suke ta rakawa, domin sune ke da “Dealership” don haka suke so da izinin Allah da taimakon Gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin Abba Kabir Yusuf da taimakon ofishin sa na mataimaki na musamman ga Gwamnan Kano a kasuwar titin Bairut, za su yi mai yiwuwa wajen samawa ‘yan asalin jihar Kano wannan “Dealership”.
Hon. Bello Jaddah Sharifai ya ce idan aka sami “dealership” ga ɗan asalin jihar Kano, yanda ake gasar harkar kasuwanci to zai taimaka wajen samun sauƙin farashin waya saboda kowane “dealership “zai so ya yi sauƙi domin a sayi kaya a wajensa, saɓanin ace ,mutum ɗaya ne yake dashi ,shi ne zai yi farashin da ya ga dama.
Sai dai ya ce wannnan kuma ba yana nufin suna ƙoƙarin yin haka bane domin tauye wani domin ba ɗan asalin jiha bane, ana so ne al’umma su sami sauƙi ,domin yanda waya ta zama abokiyar rayuwa a kowane yanayi ya zamana yan asalin Kano wacce ta zama wata babbar cibiya ta kasuwancin waya a Nijeriya da Afirka su sami dama wajen inganta harkar.
Sharifai ya ce yanzu kusan harka a rayuwa a komai ya juya ta fasahar zamani kuma a kasuwar waya ta kan titin Bairut kaso 9 ma su harkar waya duk matasa ne,cikinsu akwai masu ƙarfi da tsaka-tsaki dama na can ƙasa. A ƙarƙashin ofishin sa na mataimakin Gwamna na musamman kan kasuwar waya ta titin Bairut ma akwai shiri da suke tsarawa matasa da za a baiwa masu harkar waya ta fannoni daban-daban kama daga gyaran waya da sayar da kayan waya da masu kwamfura tallafi.
Ya ce a tsarin za a soma daga kasuwar Bairut sannan a yi a dukkan kasuwannin Kano a tantance su a ba su jari a horar da masu gyaran waya a basu kayan gyara don suma su horas da wasu, sannan masu harka da na’ura mai ƙwaƙwalwa wajen sabunta manhajar waya suma za a baiwa matasa horo akai.
Hon. Bello Jadda Sharifai ya yi kira ga ‘yan kasuwar waya na titin Bairut da cewa suna matuƙar buƙatar haɗin kai da goyon bayansu akan wannan takara da yake na shugabancin ƙungiyar kasuwar domin kai wa ga nasara da zai kawo tsare-tsare na daɗa bunƙasa cigaban kasuwar.
