Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Iyalan Marigayi Magaji Lawali wanda ake zargin kwamandan CPG na Zamfara ne ya kashe Kanar Rabi’u ‘Yandoto sun yaba wa kwamishinan ‘yan sandan jihar, Gwamna Dauda Lawal da kuma babban lauyan jihar kuma kwamishinan shari’a bisa jajircewar da suka yi wajen ganin an yi wa mahaifinsu adalci.
Alhaji Nura Lawali Magaji Yandoto ya bayyana hakan a wata tattaunawa da ya yi da Blueprint Manhaja jim kaɗan bayan kammala zaman kotun a Gusau ranar Laraba.
“Mun tashi da Mummunan lamari a gidanmu a lokacin da aka kashe mana mahaifi, Magaji Lauwali Yandoto, Wanda ya bar ‘ya’ya 23, kuma ginshiƙin al’ummarmu, wanda korarren jami’in soja kuma tsohon kwamandan rundunar kare al’umma ta jihar Zamfara, CPG, Kanal Rabiu Yandoto rtd ne ya kashe shi wasu watanni baya,” ya ce.
A cewarsa, “A yanzu haka Rabi’u Yandoto yana tsare, kuma muna da yaƙinin za a yi adalci.”
Ya yi kira ga hukumomi da su tabbatar wanda ya aikata laifin ya fuskanci fushin doka.
“A matsayinmu na iyali, an bar mu a ruguje mu 23 daya bari yanzu mun zama marayu, saboda haka muke neman ayi mana adalci a shari’ar da take gudana ba wai mahaifinmu abin kauna ba har ma da al’ummarmu, wadanda wannan rashin ya shafa,” ya ce.
“Muna yaba wa kwamishinan ‘yan sanda, ma’aikatar shari’a, da alkalan Zamfara bisa jajircewarsu wajen tabbatar da doka da adalci.”
Ya bayyana Gwamna Dauda Lawal a matsayin shugaba nagari wanda ya himmatu wajen kawo karshen rashin tsaro da jihar Zamfara ke fama da shi sama da shekaru goma.
A wata hira da jaridar Blueprint Manhaja, shugaban ƙungiyar da ke kula da masu ƙaramin ƙarfi a jihar Zamfara Malam Murtala Ibrahim Zakoli ya bayyana cewa ƙungiyar za ta ci gaba da bibiyar lamarin har sai an yi adalci ga iyalan mamacin.
Idan dai za a iya tunawa, a watan Agustan wannan shekara, wata tawagar jami’an tsaron al’ummar jihar Zamfara, CPG, sun kama Marigayi Magaji Lawali, wanda shi ne abokin siyasar Sanata Kabiru Garba Marafa a gidansa dake garin Yandoto a karamar hukumar Tsafe, kuma ya mutu a hannunsu washegari.
