Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
An bayyana Manjo Hamza Almustapha da cewa mutum ne da yake da inganci da son cigaban ƙasa da zai iya samar da kyakkyawan jagoranci da fitar da al’ummar ƙasar nan daga yanayi na ƙuncin rayuwa.
Shugaban Network for Better da ke fafutukar ganin Manjo Hamza Almustapha ya zama shugaban ƙasar Nijeriya reshen jihar Kano, Mustapha ɗahiru ne ya bayyana hakan da yake zantawa da manema labarai.
Ya ce su suna da yaƙinin Almustapha zai iya kawo sauyi a halin da ake ciki a ƙasar nan domin waɗanda suke da tunani ada na ganin ba zai iya ba yanzu sun yarda sun tabbatar zai iya cikin ikon Allah.
Ya ce da ma Hausawa na cewa Juma’ar da za ta yi kyau tun daga Laraba ake gane ta, to tuni sun gane hakan akan Almustapha suna yi masa kyakkyawan fata ko ta ina masoya sai ƙaruwa suke.
Alhaji Mustapha ɗahiru, Shugaban “Network for Better” na jihar Kano ya ce tunda suka soma wannan fafutuka akan Hamza Almustapha sai akhairi suke gani ta ko’ina ciki da wajen ƙasar nan mutane na ta addu’a akan nasarar tafiyar.
