Farfesa Sa’adatu Liman ta yaba wa Gwamna Sule kan gina hanyar kilomita 4.5 a cikin Jami’ar NSUK

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

Shugabar Babbar Jami’ar Jihar Nasarawa dake garin Keffi, hedikwatar ƙaramar hukumar Keffi a jihar Nasarawa, Farfesa Sa’adatu Hassan Liman ta yaba wa gwamnan jihar, Injiniya Abdullahi Sule dangane da kwangilar gina sabbin hanyoyi da kwalbati irin na zamani na kilomita 4 da rabi a cikin jami’ar ta jihar da ake yi a yanzu, inda ta ce tabbas idan aka kammala aikin zai je nesa ba kusa ba wajen inganta harkokin karatu da zirga-zirgar ɗalibai da malamai a jami’ar baki ɗaya.

Farfesa Sa’adatu Hassan Liman ta yabi gwamnan ne a lokacin da take tattauna da wakilin mu game da gina sabbin hanyoyin a ofishin ta dake jami’ar cikin makon nan.

Ta ce kafin yanzu gwamnan ya daɗe yana tallafa wa jami’ar a fannoni daban-daban da dama faro daga tallafin kuɗi da kayayyakin karatu da inganta tsarin karatu da koyarwa da dai sauransu a jami’ar.

A cewarta tuni waɗanda aka bai wa kwangilar aikin gina hanyoyin suka fara aiki kuma aiki na tafiya yadda ya kamata ba tare da matsalar komai ba.

Shugabar babbar jami’ar ta gwamnatin jihar Nasarawa Farfesa Sa’adatu Hassan Liman ta kuma yi kira ga duka malamai da ɗalibai da sauran ma’aikatan jami’ar baki ɗaya a duka matakai su tabbatar suna cigaba da bai wa masu aikin cikakken gudumawa don tabbatar da nasarar aiki a ƙarshe don a cewarta idan aka kammala aikin tabbas su za su mora fiye da kowa.

Farfesar har ilau yau sai ta yi amfani da damar inda ta tabbatar cewa kawo yanzu ɗinbin nasarori da aka samu a jami’ar a karkashin jagorancin ta ta iya cimma ne sakamakon cikakken goyon baya da tallafi akai-akai da ake samu daga gwamnatin ta Injiniya Abdullahi Sule inda ta buƙace shi kada ya yi sanyin gwiwa a ƙoƙarin da yake yi don tabbatar jami’ar ta cimma babbar burin ta na samar da ingantattun ilimin addini dana zamani wa dinbin al’ummar jihar dama wasu daga waje.

Wakilinmu a jihar dai kafin wannan tattaunawarsa da shugabar jami’ar ya zaga cikin jami’ar baki ɗaya inda ya gane wa idanunsa wannan aikin gina sabbin kilomita 4 da rabi na hanyoyin cikin jami’ar wadda tuni aka fara kuma ya lura aikin na tafiya cikin tsari kamar dai yadda shugabar ta bayyana.

By ukarofi