Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Kwana guda bayan Kotun Shari’ar Musulunci ta wanke Kwamishinan Jigawa Auwal Sankara, daga zargin yin lalata da matar aure, ‘yan sanda a Kano sun kama Nasir Buba, tsohon mijin wacce ake zargin tana soyayya da kwamishinan, Tasleem Baba-Nabegu.
An kama Buba ne a ƙofar ofishin lauyansa a ranar Talata.
Blueprint Manhaja ta rawaito cewa hukumar Hisbah ta jihar Kano kwanan nan ta kama Sankara ta tsare shi bayan Buba ya kai ƙarar cewa kwamishinan na neman matarsa.
Buba ya shigar da ƙara a kotun Shari’a bisa zargin.
Sai dai a zaman kotun na ranar Litinin, alƙalin kotun, Ibrahim Sarki-Yola, ya yi hukuncin wanke Kwamishinan bisa rahoton binciken da ofishin Mataimakin Sufeto Janar na ‘yan sanda, shiyya ta 1 a Kano ya gabatar.
‘Yan sanda sun bayyana cewa bisa bincikensu, ba su samu wani shaidar da za ta tabbatar da zargin zina a kan wanda ake zargi ba.
Bayan kotun ta wanke zargin, sai kuma reshe ya juye da mujiya, inda ‘yan sanda suka kama mijin matar, Buba, a ranar Talata bisa zargin yi wa matarsa kutse a wayar salular ta.
Majiyoyi sun bayyana cewa Buba ya samo bayanai da dama daga wayar matarsa don yin amfani da su wajen tabbatar da zargin da ya gabatar a kan kwamishinan.
“Gaskiya abin ya nuna cewa ‘yan sanda suna da ɓangaranci a wannan lamari. Nasir ya gabatar da hotuna, bidiyo, saƙonnin rubutu da muryoyi da ke nuna hujjar alaƙar soyayya tsakanin kwamishinan da matar,” in ji wata majiya da ke da masaniya game da al’amarin.
“Abin mamaki ne yadda ‘yan sanda suka wanke kwamishinan sannan suka kama wanda ya kai ƙarar bisa zargin ɓata suna ta yanar gizo.”
Da aka tuntuɓe shi, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kano, Abdullahi Kiyawa, ya ce ba a sanar da shi wannan ci gaban ba.
