A ranar Litinin da ta gabata, 11 ga Nuwamba, 2024 Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya bayyana, dole ne duniya ta yi ƙoƙarin kawo ƙarshen hare-haren Isra’ila a Gaza, inda ya ce, babu wani burin siyasa ko dabarun soji ko kuma na tsaro da za a fake da su wajen hallaka rayukan mutanen da basu ji ba ba su gani ba, shugaban ya bayyana matuƙar damuwarsa kan yaƙin kisan ƙare dangi da Isra’ila ke ci gaba da yi a zirin Gaza, wanda kuma ya nuna matuƙar damuwa kan yadda yaƙin faɗaɗa zuwa Lebanon.
Yaƙin da aka yi da manufar murƙushe Hamas da Hizbullah daga Falasɗinu da Lebanon, ya haifar da bala’i a ɓangaren harkokin jin ƙai, musamman a Gaza. An kira taron kolin ne na Riyadh ne domin tunkarar lamarin da ke da tasiri mai yawa ba a yankin gabas ta tsakiya kaɗai ba har ma da duniya baki ɗaya.
Tinubu ya halarci taron na yini ɗaya a matsayin jagoran Nijeriya, wanda ya daɗe yana cikin ƙungiyar OIC, tare da wasu shugabannin ƙasashe da gwamnatoci na OIC da ƙungiyar ƙasashen Larabawa. Tinubu ya yi gargaɗin cewa “rikicin Falasɗinu ya daɗe sosai, kuma yana jawo wahalhalu marasa iyaka, ba za a bari hakan ya ci gaba ba,”
Dangane da manufofin Nijeriya na ƙetare, shugaban ya yi kira da a gaggauta tsagaita buɗe wuta a Gaza tare da jaddada goyon bayan Nijeriya ga samar da ƙasashe biyu, inda Isra’ila da Falasɗinawa za su kasance tare cikin tsaro da mutunci. Ya yi nuni da cewa, wannan mafita ta kasance wani ɓangare mai amfani ga dauwamammen zaman lafiya a yankin.
A cewarsa, “Rikicin Falasɗinu ya daɗe yana ci gaba da jawo wahalhalu marasa adadi ga mutane da dama. A matsayinmu na wakilan al’umma masu darajanta adalci, mutunci, da kuma ƙimar rayuwar ɗan Adam, muna da haƙƙin na mu kawo ƙarshen wannan rikicin. Ba zai wadatar ba in muka tsaya Allah wadai kaɗai. Dole ne duniya ta yi aiki don ganin an kawo karshen ta’addancin da Isra’ila ke yi a Gaza, wanda ya ƙi ci yaƙi cinyewa. Babu wata manufa ta siyasa, ko dabarun soji, ko kuma rashin tsaro da ya kamata ya bada damar salwantar da rayukan da ba su ji ba basu gani ba.”
Shugaban ya buƙaci ɓangarorin da ke rikici da su mutunta ƙa’idojin haƙƙin ɗan adam, daidai da tsarin shari’a da diflomasiyya na duniya, yana mai cewa, “Taimakon jin ƙai ba gata ba ne, haƙƙin ɗan adam ne. Babu wani mutum ko dan ƙasa ne, ko wata ƙabila, ko wani addini, da za a hana shi samun tallafin a lokutan rikici. Dole ne kuma mu tabbatar da cewa ma’aikatan jin kai dake gaba-gaba suna cikin aminci da koshin lafiya don gudanar da aikinsu a Gaza.”
Batun samar da ƙasashe biyu, a cewar Tinubu, wani haske ne na sabon fata, wanda ke wakiltar haƙƙokin Isra’ilawa da Falasɗinawa na ’yancin kai da zaman lafiya.
Ya ƙara da cewa: “Samar da zaman lafiya a tsakanin ƙasashen biyu, ya kasance wani ginshikin ne na sabunta fata, wanda ke wakiltar hakkokin Isra’ila da Falasɗinawa na tabbatar da ‘yancin kai da zaman lafiya. Ba batun diflomasiyya kawai bane; hangen nesa ne da ake son tabbatar da shi bisa ƙa’idojin daidaito da fahimtar juna. Cimma wannan hangen nesa yana buƙatar sadaukar da kai don tattaunawa da mutunta tarihi. Dukanmu mun san cewa wannan rikici bai fara ba a ranar 7 ga Oktoba 2023. Za a iya warware shi ta hanyar sasantawa bisa ƙa’ida, da kyakyawar fahimta.”
Ana iya ganin yadda Tinubu ya yi nuni da daidaito don dakatar da bala’in da ake fuskanta a Gaza. Isra’ila ta kashe Falasɗinawa sama da 43,736 ya zuwa yanzu, tare da raunata 104,000, yayin da aƙalla mutane 11,000 ba a ji ɗuriyarsu ba, waɗanda ake kyautata zaton sun mutu a ƙarƙashin ɓaraguzan gidajensu a duk faɗin yankin.
Bankin Duniya ya ce, an lalata gidaje 100,000. Haramcin da Isra’ila ta yi wa Hukumar Ba da Agaji da Ayyuka ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA) daga kai kayan agaji ga Falasɗinawa da ‘yan gudun hijira a Labanon na da nufin ɗaukar gallaza wa mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.
Wani kwamiti na musamman na Majalisar ɗinkin Duniya da ya binciki al’adun Isra’ila ya faɗa a cikin wani sabon rahoto da ya fitar makonni biyun da suka gabata cewa, abin da Isra’ila ke yi a Gaza yana da dukkan siffofi na kisan ƙare dangi. Ya gano cewa a farkon shekarar 2024, an jefa sama da tan 25,000 na bama-bamai daidai da bama-baman nukiliya guda biyu a zirin Gaza, wanda ya haifar da mummunar illa da rugujewar tsarin ruwa da tsaftar muhalli, ɓarnata amfanin noma, da gurɓacewar yanayi.
Yayin da kwamitin na musamman ya miƙa rahotonsa ga zauren Majalisar Dinkin Duniya a ranar Litinin ɗin da ta gabata, idan kuma aka yi la’akari da abin da ke sama, abin kunya ne kuma jahici irin yadda wasu ’yan Nijeriya ke nuna adawa kan tsoma bakin Tinubu a rikicin Gaza, inda suka ce a maimakon haka wai kamata ya yi ya goyi bayan kisan ƙare dangi. Abin baƙin ciki ne irin yadda wasu ke kallon lamarin da tsattsauran ra’ayi na addini duk da cewa Isra’ila ba ƙasar al’ummar Kirista ba ce, kuma ta lalata dukkan coci-coci tare da kashe yawancin Kiristoci a Gaza.
A cikin gurɓataccen tunaninsu, sai suka yi kamar ba su san cewa tun fil’azar Nijeriya ba ta da wata alaƙa ta diflomasiyya da yankin Yahudawan sahyoniya, har sai da shugaban ƙasa Ibrahim Babangida wanda Musulmi ne shi ya mayar da ita. ƙasar Afirka ta Kudu, wacce za ta iya da’awar cewa ta fi mu yawan al’ummar Kiristanci, ta kasance a sahun gaba wajen gurfanar da Isra’ila gaban kotu a kotun hukunta manyan laifuka ta ƙasa da ƙasa (ICC), wadda ta tuhumi gwamnatin sahyoniyawan da aikata laifukan yaƙi a Gaza. Nijeriya ƙarƙashin Tinubu ta yi daidai kan kokawa mai tsanani kan cin zarafin da Isra’ila ke yi.
Yayin da muke yaba wa Shugaba Tinubu kan matsayinsa, muna roƙonsa da ya ƙara ƙaimi wajen kiransa ta hanyar shiga ƙawancen ƙasashe da ƙungiyoyi don ba wai kawai ya hana Isra’ila sukuni ba ne, amma ya ba da damar gurfanar da gwamnatin Netanyahu a gaban kuliya kamar yadda kotun ICC ta zarge ta. Matsayin nasa ya yi daidai da na Yarima mai jiran gado na Saudiyya Mohammed bin Salman, wanda ya yi Allah-wadai da zaluncin Isra’ila. Bai kamata Nijeriya ta yi ƙasa a gwiwa ba a kan nuna matsayarta a diflomasiyya.
