Zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Donald Trump ya sanar a ranar Juma’a cewa, mai magana da yawun yaƙin neman zaɓe, Karoline Leavitt, ‘yar shekaru 27, za ta yi aiki a matsayin sakatariyar yaɗa labaran fadar White House.
Leavitt “tana da haifin yunani, mai juriya ce, kuma ta tabbatar da cewa, ta iya hulɗa da jama’a. Ina da cikakken kwarin gwiwa cewa za ta yi fiye da tsammanin mu, kuma zata taimaka wajen isar da saƙonmu ga jama’ar Amurka,” inji Trump a cikin wata sanarwa.
Karoline Leaɓitt za ta zama ɗaya daga cikin matasa masu ƙarancin shekaru da suka riƙe muƙamai masu mahimmanci, wato aiki a matsayin fuskar Fadar White House, a matsayin mai watsa labarai da amsa tambayoyin da suka shafi fadar White House.
Ta yi aiki a matsayin sakatariyar yaɗa labarai ta ƙasa ga Trump a lokacin yaƙin neman zaɓensa, inda a watan Yuli ta haifi ɗanta na farko gabanin zaɓen, kamar yadda ta shaida wa wani gidan talabijin na Foɗ News da aka buga ta yanar gizo ranar Juma’a.
Bayan ta yi aiki a matsayin mataimakiyar sakatariyar yaɗa labarai ga Trump a wa’adinsa na farko a kan karagar mulki, ta fito takarar kujerar ‘yar majalisar wakilai daga jiharta ta New Hampshire a shekarar 2022, saidai ba ta yi nasara ba a zaɓen.
Ta kuma yi aiki a matsayin darektan sadarwa ga ‘yar majalisa Elise Stefanik, wacce Trump ya zaɓa ta zama jakadiyar Majalisar Dinkin Duniya.
“Ban girma a cikin gidan siyasa ba. Na girma kamar yawancin Amurkawa, wato a cikin gidan matsakaitan ‘yan kasuwa a nan a jihata ta New Hampshire,” ta gaya wa Fox News podcast.
Ta kuma ƙara da cewa, “Na tsunduma cikin harkar siyasa a lokacin da nake kwaleji ta Kwalejin Saint Anselm, a Manchester (New Hampshire).”
