Jagoran ‘yan adawar jamhuriyar Somaliland mai cin gashin kanta, Abdirahman Mohamed Abdullahi, ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a yankin.
Mutumin wanda aka fi sani da Irro, ya samu kashi 64% na ƙuri’un da aka kaɗa, wanda ya ba shi damar zama shugaban ƙasar Somaliland na shida tun bayan rabuwar ta da ƙasar Somaliya a shekarar 1991.
Dan shekaru 69, wanda tsohon kakakin majalisar dokokin Somaliland ne, ya doke Musa Abdi Bihi mai ci, wanda ya samu kashi 35% na ƙuri’un da aka kaɗa.
A lokacin yaƙin neman zaɓe, Irro ya ce, jam’iyyarsa za ta sake duba yarjejeniyar da ta haifar da cece-kuce na ba da hayar wani ɓangare kusa ga ƙasar Habasha mai nisan kilomita 20 da su, na tsawon shekaru 50 don kafa sansanin sojin ruwa yarjejeniyar da ke haifar da rikici a yankin.
A wani ɓangare na yarjejeniyar da aka sanar a ranar sabuwar shekara, Somaliland na sa ran Addis Ababa ta amince da ita a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta.
Wanda hakan ya harzuƙa ƙasar Somaliya, wadda ta ɗauki Somaliland a matsayin wani yanki na ƙasarta, kuma ta ce tana kallon yarjejeniyar a matsayin wani zalunci.
Irro bai taɓa yin watsi da yarjejeniyar ba, amma a lokacin da ake tattaunawa ya yi amfani da kalaman diflomasiyya, wanda ke nuni da cewa za a sauya salo.
Somaliland dai na cikin wani yanki mai matuƙar muhimmanci na duniya, kuma ana kallonta a matsayin wata kofa ta mashigin tekun Aden da kuma Tekun Bahar Maliya.
Duk da kwanciyar hankali da aka samu da kuma zaɓukan dimokuraciyya na yau da kullun, hakan bai sa ƙasar a jerin ƙasashe da duniya ta san da su ba.
“Dukkanmu mun yi nasara, jihar Somaliland ce ta yi nasara,” inji Irro, yayin da yake yaba wa kowa da kowa kan gidanar da zaɓe cikin lumana wanda da aka gudanar a ranar 13 ga Nuwamba, da har jami’an diflomasiyya daga kasashen Turai ciki har da Amurka suka halarta.
Ya kuma gode wa shugaban ƙasa mai barin gado, wanda ya jagoranci yankin tun a lokacin rabuwar sa da uwar gidansa a shekarar 2017.
‘Yan adawa sun ce, Bihi ya sha kaye ne sakamakon irin salon tafiyar da mulki da ya ɗauka. Su na masu cewa, ya yi watsi da ra’ayin jama’a ne a daidai lokacin da matsalolin tattalin arziki suka durkusar da darajar kuɗin ƙasar.
Ana dai kallon zaɓaɓɓen shugaban da za a rantsar a ranar 14 ga watan Disamba a matsayin wani tsani da zai kai ƙasar gaba da kuma ƙara haɗa kai al’umma.
