Za mu yi amfani da tallafin da NITDA ta bamu wajen ci gaban matan Kannywood – Mansurah Isah

Spread the love

DAGA MUKHTAR YAKUBU

A sakamakon tallafin da Mansurah Isah ta samu daga National Information Technology Development Agency (NITDA) ta sha alwashin kawo sauyi a masana’antar domin su samu su ma su dogara da kansu a maimakon su tsaya suna fitowa a matsayin jarumai, wanda kuma daga an daina yayin su ko suka yi aure kuma shi kenan sana’ar ta su ta tsaya, don haka take ganin a yanzu dama ta samu da za su koyar da mata duk wasu harkoki na sana’ar fim don a kawar musu da tunanin cewar sai aktin kawai za su iya. 

A cikin tattaunawar da wakilinmu ya yi da ita, Mansurah Isah ta bayyana yadda ta samu wannan tallafin daga Gwamnatin Tarayya da kuma hanyoyin da ta bi don ganin an cimma nasarar samun su, kuma burin da take da shi don ganin masana’antar Kannywood ta ci moriyar wannan tallafin, don haka sai ku biyo mu ku ji yadda hirar ta kasance.

MANHAJA Mansurah Isah mun samu labarin wani tallafin kayayyakin bunƙasa harkar fim da kika samu daga Gwamnatin Tarayya ta ƙarƙashin National Information Technology Development Agency (NITDA). Masu karatunmu za su so jin yadda aka samu wannan tallafin da kuma yadda za ku yi amfani da shi don bunƙasa harkar fim.

MANSURAH ISAH: To da farko bayan sallama zan gabatar da kaina a matsayin jaruma, furodusa, darakta, kuma a matsayina na mace a cikin Kannywood duba da yadda maza ne suke da ƙarfi a kowanne ɓangare na harkar zan iya cewa ma sun mamaye komai, saboda furodusa ɗin za ka ga duk maza ne darakta da sauran ɓangarori za ka ga duk maza ne. To wannan abin ya sa na zauna na yi nazari na ga to mu matan nan me muke yi ne. Kuma duk wata mace idan ta zo harkar fim ba ta da wani tunani sai na ta zama jaruma, duk da cewa akwai ɗumbin arziki a cikin harkar ta hanyoyi da dama a cikin harkar wanda mu mata sam ba ma kula da shi ko ba mu san da shi ba. Sai ya zama mu burin mu mu zo mu sayar da kyaun fuskar mu da kyaun jikinmu a saka mu a fim mu yi kuɗi mu samu ɗaukaka, kuma daga lokacin mu ya wuce an daina yayin mu wata ta zo ana yayin ta sai kuma mace ta shiga cikin wani irin yanayi, ko ta fara shaye shaye, ko ta dawo ci da sha ma ya gagara, har ma ta kai duk inda ta je ma ana korar ta saboda ba ta da wani amfani lokacin ta ya wuce don ba ta da wata damar da za ta bai wa harkar fim ɗin kariya lokacin ki ya ƙare. 

Amma mazan za ka ga sun ɗauki tsawon lokaci a matsayin masu gudanar da rayuwa su a cikin harkar fim, ko mutum ya kasance a matsayin furodusa ko darakta ko mai ɗaukar hoto da sauran su, kuma za a daɗe ana damawa da su. Ga su nan da yawa da muka sani a yanzu sun yi kuɗi sun zama furodusa ɗin kansu, har ma ‘ya’yansu sun gaje su.

Amma mu mata, sai ka ga mace ta yi aure daga nan matsayin ta ta jaruma ya ƙare . To me mace za ta iya yi bayan ta yi aure a cikin harkar fim, don za ka ga yawancin auren ma da muke yi na sha’awa ne ake yi mana. Namiji ne zai aure mu ba don wai yana son mu tsakani da Allah da Annabi ba, sai don samun wata biyan buƙatar sa. Wanda kuma daga kin yi auren za ki shiga wani irin yanayi na ƙuncin rayuwa. Domin mu mata muna da taushin zuciya wadda ko da mutum ya zo mana da mummunan hali ba za mu gane ba, tun da mun ɗauki zuciyarmu da soyayyarmu mun ba shi, sai mu rinƙa kallon kamar shi ma haka yake yi mana. Ko kuma ka ga ‘yar fim ta yi aure ta shiga cikin wani irin garari, saboda ta saba ta yi aiki ta samu kuɗi kuma ta yi aure a yanzu ba ta aikin komai don haka babu inda kuɗi zai shigo mata, kuma babu mamaki mijin da ta aura ba mai ƙarfi ba ne, irin wannan sai ka ga aure ya mutu.

To wannan dalilin ne ya sa na yi ƙoƙari na nemi na samu ganin shi babban darakta na NITDA, kuma na yi sa’a aka ba ni lokaci muka je da ni da wata ƙawata na bayar da duk wasu bayanai na da kuma buƙatar da muke da ita a masana’antar Kannywood, na yi musu bayani a kan yadda mu mata muke bukatar taimako a masana’antar Kannywood, domin ceto rayuwarmu daga mamayar da maza suka yi mana, wanda a dalilin wannan mamayar da maza suka yi mana za ka ji yarinya tana cewa da ta zo an kaita wajen wane ya je ya ce zai kwana da ita, to irin wannan mamayar da maza suka yi ne yake kawo hakan, saboda mata ba su da ƙarfin da maza suke da shi.

Yanzu da na fara furodusin har na fara samar da manyan jarumai, kuma a yanzu kusan kullum sai mata sun kira ni a kan suna son ‘ya’yansu su shigo harkar fim amma suna son su shigo ta hannuna saboda ni mace ce ‘yar uwar su kuma babu abin da zan yi na illata rayuwar su, don dole su bi dokokina yadda za su yi komai cikin sauƙi, don za ka ga wasu da gaggawar su suke zuwa su kai ga buƙatar su ba sa son jira. 

To duk irin wannan bayani na yi musu kuma suka muhimmancin abin da nake da burin yi, don haka suka ce na zo na rubuta duk abubuwan da nake buƙata wanda ni ma zan zama wata a cikin harkar fim ɗin domin a samu a ɗaga darajar mata a Kannywood a kan mataki na ci gaban zamani. Duk da harkar gwamnati ce mun ɗauki tsawon wata biyar muna cike-ciken takardu da bibiya, har lokacin da muka yi nasara aka kira ni aka ce kayana ya iso kuma za a kawo shi Kano.

Alhamdulillah kaya ya zo, kuma duk wani abu da na rubuta muna buƙatar sa an ba mu , a yanzu muna so mu samar da babban waje da zai zama wajen gudanar da aikin, saboda wajen da muka tanada kafin zuwan kayan sai da kayan ya zo muka ga wajen ya yi kaɗan don haka saboda yanayin tsaro dole ta sa za mu sauya waje. Kuma duk kayan da suka ba mu su ne dai wanda ake aiki da su a yanzu a duniya babu wani tsoho kayayyakin duk wani aikin da za a yi a masana’antar Kannywood da akwai shi a ciki tun daga kyamara, kwamfiyuta, da duk wani abu da ake amfani da shi a harkar fim ta duniya, gaskiya an yi niyyar a tallafa wa harkar fim ɗin Kannywood don ɗaukaka darajar mata don su ma su samu sana’ar su ta kansu ba wai aktin kawai ba.

By ukarofi