Hamdiyya Sokoto: Wacce rawa matasa ke takawa a zaurukan sada zumunta?

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Labarin zargin cin zarafin wata matashiya ‘yar Jihar Sakkwato, Hamdiyya Sidi Sharrif, da ake yi wa Gwamnatin Jihar Sakkwato da jami’an tsaro, na cigaba da ɗaukar hankalin ‘yan Nijeriya, musamman matasa da ƙungiyoyin mata, da masu kare haƙƙokin ɗan adam. Yayin da ake cigaba da yin Allah wadai da abin da ake zargin ‘yan koren gwamnati sun yi mata na duka da wulaƙanci, saboda ta yi wani bidiyo da ya yaɗu sosai a zaurukan sada zumunta, inda take zargin Gwamnatin Jihar Sakkwato da jami’an tsaro da gaza ɗaukar mataki kan halin da ake ciki na taɓarɓarewar tsaro a jihar. A maimakon a yaba mata a matsayinta na matashiyar mace da ta nuna damuwa da kulawa kan halin da mata da yaransu a ƙauyukan jihar ke ciki, da kuma yadda rayuwar waɗanda ke zaman gudun hijira a cikin garin Sakkwato ta shiga wani yanayi marar daɗi, sai ‘yan koren gwamnati da muƙarrabanta, har da wasu malaman addini, suka riƙa sukar maganganunta ana juya batun da sunan ta yi wa Gwamnan Sakkwato, Ahmad Aliyu, rashin kunya.

A maimakon a dubi saƙon da take isarwa, don gwamnati ta ƙara ƙaimi kan ƙoƙarin da take cewa tana yi a harkar tsaro, har ma ƙila a yaba wa gudunmawar da jama’ar jihar ke bayarwa na shawarwari da bayanan sirri, sai aka nemi mayar da abin siyasa, har da jefa rayuwar Hamdiyya cikin mugun yanayi, da ake neman ɗaukar ranta. Bayan tsare ta da ‘yan sanda suka yi na wani lokaci, don tsorata ta da rufe mata baki. Wannan abin da suka yi kuma shi ya ƙara fitar da batun da ake yi na tauye wa jama’a ‘yancinsu na faɗin albarkacin baki, a yanayin da ake ciki na lalacewar tsaro. Sannan matakan da ake ɗauka akan yarinyar ya ƙara sa ta zama marar tsoro kuma sunanta ya ƙara fita a duniya, a matsayin wacce ake zalunta, don ta yi magana a yanar gizo! A yayin da wasu ‘yan mata da, samari ke can tiktok da Facebook suna rawar baɗala da maganganun batsa, suna zubarwa kansu mutunci da iyayensu.

Ni da kaina na ga wani bidiyo da ta sake fitarwa bayan ta samu sauƙin dukan kawo wuƙa da aka yi mata, tana ƙalubalantar Gwamnan jihar bisa yunƙurin kasheta da ta yi zargin yana da hannu a ciki.

Manufar rubutuna ba duba ko abubuwan da ta yi zargi a kansu haka ne ko ba haka ba ne, amma dai ina so ne mu duba ƙalubalen da ake samu game da yadda matasa ke amfani da zaurukan sada zumunta, da kuma tasirin su. Ba kamar a baya ba, a yanzu jami’an tsaro suna sa ido sosai ga abubuwan da jama’a ke rubutawa su yaɗa a shafukansu na manhajojin sada zumunta.

Idan za mu iya tunawa tun a shekarar 2019 da Majalisar ƙasa ta amince da kafa dokar da za ta yi yaƙi da yaɗa labaran ƙarya da bayanan da za su iya zama haɗari ga al’umma, ake ta samun ƙorafe-ƙorafe daga ‘yan Nijeriya da ƙungiyoyin ƙare ‘yancin ɗan adam, game da tanade-tanaden dokar da yadda za a iya amfani da ita a murƙushe mutane masu bayyana ra’ayoyinsu. Kamar dai yadda muke iya gani yanzu. Kodayake ba ina nufin kafa doka don yi wa mutane dabaibayi ko linzami game ayyukansu da abubuwan da suke yaɗawa kuskure ba ne, lallai akwai buƙatar sa ido sosai, don inganta tsaro da zaman lafiya da kiyaye haƙƙokin jama’a, matuƙar za a kiyaye da haƙƙokin ɗan adam. Amma kafa doka don a takurawa mutane da hana su sakewa ko faɗar gaskiya bai dace ba.

Sannan kuskure ne jami’an tsaro su bari ‘yan siyasa na amfani da su wajen farmakar waɗanda ake kallo a matsayin ‘yan adawa, ko masu ƙalubalantar manufofin gwamnati. Har yanzu ba mu manta da ɓacewar matashin nan ɗan Kaduna da ake kira Abubakar Idris Dadiyata ba, wanda har kawo yanzu da nake wannan rubutun ba a san a inda yake ba. An zargi jami’an tsaro da ɗauke shi su kai shi wani ɓoyayyen waje, don rufe masa baki kan irin rubuce-rubucen da yake yi, da a ciki yake yawan sukar wasu tsare-tsare da manufofin gwamnati. Tun a ranar 1 ga watan Agusta na shekarar 2019, da aka tafi da Dadiyata, har kawo yanzu babu shi babu labarinsa.

Labarin Hamdiyya da Dadiyata ya kusa zuwa ɗaya, kodayake ita har kawo yanzu tana gidan iyayenta, tana shaƙar iskar ‘yanci. Alhalin shi kuwa Dadiyata babu ma tabbas ɗin ko yana raye. Rahotanni da dama suna bayyana irin yadda ake amfani da jami’an tsaro, akan mutane masu sukar gwamnati ko ‘yan siyasa. Ko a watannin baya ma sai da aka riƙa yaɗa labarin cin zarafi da wasu jami’an soji a Jihar Zamfara suka yi wa wani mai amfani da zaurukan sada zumunta, saboda ya ƙalubalanci gwamnati game da matakan da take ɗauka kan ‘yan bindiga a jihar.

Amfani da ƙarfin hukuma ko bakin bindiga ko ‘yan bangar siyasa, a toshe bakin mai faɗar ra’ayinsa kan wata magana ko wani al’amari da yake faruwa a jiharsa, yana zubar da kimar gwamnati da jami’an tsaro. Ana ganin hakan a matsayin nuna son zuciya ko tauye haƙƙin faɗin albarkacin baki, wanda ya saɓa wa, dokokin ƙasa da tanadin Majalisar ɗinki Duniya. Yana da kyau a riƙa nazari da bin wasu hanyoyi na ƙaryata maganganun da ba na gaskiya ba, ko fayyace zarge-zargen da ake yi wa gwamnati, wanda ita take tunanin ba a yi mata adalci ba.

Duk da zargin tauye haƙƙin da ake zargin gwamnati da jami’an tsaro na yi kan masu sukar gwamnati, dole ne kuma a yaba musu ta wani ɓangaren saboda yadda suke ƙoƙarin daƙile masu amfani da zaurukan sada don hassala rikici ko tashin hankali. Kamar yadda aka yi ram da wani matashi mai suna Suleiman Yakubu da ya yi wa kansa bidiyo yana kira ga matasa su ɗauki doka a hannu wajen yin fashe-fashe da ƙone-ƙone a cikin garin Jos, a lokacin zanga-zangar tsadar rayuwa da aka gudanar a wasu sassan ƙasar nan cikin watan Yuli da ya gabata. Kun ga wannan abu ne da ya dace, domin daƙile ɓarna da inganta tsaro.

A yayin da nake jan hankalin hukumomi a Jihar Sakkwato da masu faɗa a ji na jihar su tabbatar da tsare ‘yanci da mutuncin wannan baiwar Allah Hamdiyya, da bi mata haƙƙinta na cin zarafin da aka yi mata, ina kuma kira ga matasa su guji amfani da zaurukan sada zumunta ta hanyoyin da ba su dace ba. A kaucewa cin mutuncin manya ko aibata su, a nisanci yaɗa jita-jita da labaran ƙanzon kurege, ko jirkita bayanan gaskiya, da nufin cimma wata manufa ta siyasa ko son zuciya. Lallai mu sani yanzu fa ba da ba ne, akwai dokoki masu tsauri a ƙasar nan game da masu amfani da zaurukan sada zumunta suna yin abubuwan da basu kamata ba. In kunne ya ji an ce gangar jiki ta tsira.