Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Alhaji Sani Baba, shugaban masu sayar da taki da sauran kayan amfanin gona na gidan Aminu ɗantatta a kasuwar Galadima, kuma shugaban NNPP na mazaɓar Dala, ya bayyana shugaban ƙaramar hukumar Dala, Hon. Suraj Imam da cewa mutum ne mai ƙoƙari da kowa ya san shi a haka.
Ya bayyana hakan ne da yake zantawa da ‘yan jarida a taron rantsar da kansiloli masu gafara da aka yi a sakatariyar mulki ta Dala. Ya ce kuma Allah ya taimaka ya kawo waɗanda za su yi aiki da shi jajirtattu matasa da aka ɗora kwarya a gurbinta.
Shugaban jam’iyyar NNPP na mazaɓar Dala ya yi fatan yadda aka zaɓo kansilolin da masu bai wa shugaban ƙaramar hukumar Dala shawara da sauran ma’aikata Allah ya sa su riƙe amana su kuma samu shawara na gari daga jama’a.
Alhaji Sani Baba ya ce a tsarin Kwankwasiyya dama sun saba ganin rikice-rikice da ake ƙullowa domin kawai a dakushe tasiri da ƙaruwar jagora kuma wannan ma rikicin ƙarami ne a ciki kuma duk wannan ba zai taɓa musu tasirin siyasar Kwankwaso a Dala ba ko ya kawo musu naƙasu ba.
