Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi, a ranar Litinin, ya ce, ba zai bari shaci-faɗin mutane da ake yaɗawa cewa ba sa ga maciji da ministan tsaro, Muhammad Badaru, ya shafe shi ba.
Badaru shi ne tsohon gwamnan jihar Jigawa wanda ya gama ya miƙa wa Namadi a shekarar 2023.
Gwamnan Namadi ya ce ya yi mamakin yadda aka samu wasu -wasu bayan ya tafi hutun na ƙarshen shekara na kwanaki 18 – suna ƙoƙarin ƙulla gaba a jam’iyyarsu ta APC.
Mai magana da yawun gwamnan, Hamisu Gumel, ne ya bayyana hakan, inda gwamnan ya ƙara da cewa; “A lokacin da ba na nan, abubuwa da yawa sun faru. Mu a jihar Jigawa jam’iyyarmu ɗaya, APC. Kuma a shirye nake na cigaba da tattalin wannan haɗin kai da muke da shi. A matsayina na shugaba, dole ne na mai da hankali ga abin da ya fi muhimmanci.
“Haka kuma akwai buƙatar mu kasance masu haƙuri da juna. A kodayaushe akwai mutanen da suke so su hana ruwa gudu, musamman idan suka ga ana samun cigaba kuma ba irin wadda suke so ba. To, sai su yi ta ƙoƙarin ganin sun haifar da fitina da rashin zaman lafiya. Dole ne mu tura wa waɗannan mutane aniyarsu,” in ji gwamnan.
Namadi ya kuma jaddada muhimmancin haɗin kai a cikin jam’iyyar APC inda ya yi kira ga ‘ya’yan jam’iyyar kan su guje wa duk wani abu da zai kawo hargitsi.
Gwamna Namadi ya ce duk da na tafi hutu, a kodayaushe ina cikin tattaunawa da mutane kan abubuwa na cigaba ga jihar nan da samun masu zuba hannun jari daga Gabas tsakiya.
“E, hutu ne na ƙarshen shekara, amma ina aiki a yayin da nake hutun. A wannan lokaci akwai tattaunawa mai yawa da na yi da muƙarrabaina ta hanyoyin amfani da intanet.”
Sannan ya ce wasu daga cikin masu zuba hannun jarin sun yi alƙawarin zuwa jihar nan ba da daɗewa ba, musamman waɗanda ke son shiga harkar noma. Wasu kuma suna sha’awar zuba hannun jarinsu ne a ɓangaren samar da mahauta ta zamani wanda zai bunƙasa tattalin arziƙin jihar.
Gwamnan ya ce waɗancan su ne kaɗan daga cikin abubuwan da ya yi a lokacin da yake hutunsa na kwanaki 18.
Gwamnan, a yayin dawowarsa daga hutu, ya samu tarba daga magoya bayan jami’iyyar APC a jihar waɗanda suka taru a kan titin zuwa gidan gwamnati da ke Dutse.
