Tinubu da Buhari ne suka jefa Nijeriya cikin tsananin fatara da rashin tsaro – Obasanjo

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon Shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya bayyana Nijeriya a matsayin ƙasar da ta gaza sakamakon shugabancin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari da kuma Shugaba Bola Tinubu.

Obasanjo ya ce, Tinubu da Buhari ne suka jefa Nijeriya cikin halin yunwa da rashin tsaro da rashin cigaba.

Obasanjo na waɗannan kalamai ne a yayin taron tunawa da marigayi, Chinua Achebe da ake duk shekara domin tun wa da shi wanda aka yi a jami’ar Yale da ke Amurka.

Tsohon shugaban ƙasar ya gabatar da wanj jawabi wanda aka naɗa, sannan aka kunna a wurin taron.

Haka kuma Obasanjo ya caccaki shugabanni biyu ta hanyar amfani da sunan da alumma suke kiran su da su na shaguɓe, wato: “Baba-go-slow” ga tsohon shugaban ƙasa Buhari da “Emilokan” ga Shugaba Bola Ahmad Tinubu.

“Kamar yadda za mu iya gani kuma mu fahimta, halin da ake ciki a Nijeriya ya yi muni sosai. ƙasa na daɗa lalacewa da kwatankwacin yadda ake samun ƙaruwar cin hanci da rashin tarbiyya.

Daga nan ne ake samun tashe-tashen hankula da matsalar tsaro da rarrabuwar kai da fargaba da makamantansu.

Waɗannan shugabanni biyu su ne suka jefa Nijeriya cikin mawuyacin halin a cewar shugaba Obasanjo.

Obasanjo ya zargi ɓangaren shari’a da haɗa kai da ‘yan siyasa wajen riƙe makoshin Nijeriya.

Ya soki lamarin kalmar “ka je kotu” ko mu haɗu a kotu da ‘yan siyasa ke faɗa idan an samu ƙin amincewa da sakamakon zaɓen da ya ayyana su a matsayin wadanda suka yi nasara.

Ya ce waccen jimla na nuna yadda aka kotuna suka zama ‘yan amshin shata saboda tuni wasu alƙalan ‘yan siyasa sun siye su. Kuma su ma suna aiki ne ga wanda ya fi biyansu.

Sannan Obasanjo ya koka game da mallaka wa kansu dukiya masu mulki ke yi wanda shi ma ke taimakawa wajen ruguje tattalin arziƙin ƙasa.

Sannan ya soki yadda gwamnonin suke mallake jihohin inda ya buga misali da wani gwamna da ya mallake jiharsa na tsawon shekaru 25.

Manhaja ta duba wannan al’amari inda ta fahimci, Obasanjo da shugaba Tinubu yake, domin shi ne gwamnan da tun 1999 yake da tacewa a jiharsa ta Legas.

Sannan Obasanjo da Tinubu mutane da ba sa ga maciji musamman tun bayan saɓanin da aka samu a lokacin da Obasanjo yake shugabancin ƙasa, shi kuma Tinubu yake gwamnan Legas.

Shugaba Tinubu ne kaɗai a lokacin shugaban da yake ɗan jami’iyyar AD da ke mulki bayan gaza ka da shi da jam’iyyar PDP mai mulki ta yi a zaɓen 2003.

Kusan sau ɗaya suka taɓa zama a inuwa ɗaya, wato lokacin zaɓen 2015 inda suka ƙalubalanci Shugaba Goodluck Jonathan tare da mara wa ɗan takarar shugaban ƙasa a lokacin, Muhammadu Buhari.

Haka kuma Obasanjo ya zargi yan siyasa da yin amfani da talauci da yunwa wajen samun ƙuri’u a lokacin zaɓe ta hanyar jefa al’umma a yunwa da sace kuɗinsu, sannan a zago lokacin zaɓe a raba wa masu zaɓe abinci.

Lissafin shi ne duk shugaban da ya fi kawo abinci ko kuɗi mai yawa, shi al’umma za su bi.

Sannan ya koka game da yawan yaran da ba sa zuwa makaranta da matsalar tsaro da cin hanci da rashawa inda ya ba da shawarar ya kamata a yi koyi da tsarin tafi da gwamnati irin na ƙasashen Japan, Kudancin Korea, da Singapore domin samun cigaban.

By ukarofi