Sarauniyar kyau ta Nijeriya, Chidimma Adetshina ta ƙare a mataki na biyu a gasar sarauniyar kyau ta duniya ta 2024 da aka gudanar karo na 73.
Wakiliyar ƙasar Denmark, Victoria Kjaer Theilvig ce ta zo ta farko a gasar da aka gudanar a birnin Meɗico City na ƙasar Meɗico.
A cikin watan Agusta ne aka zaɓi Chidimma a matsayin sarauniyar kyau ta Nijeriya, bayan ta fice daga takarar gasar a Afirka ta Kudu saboda matsalolin da suka taso kan asalinta.
Mutum 125 ne suka shiga gasar sarauniyar kyau ta duniya a bana, ciki har da wakilan ƙasashen Iran da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Somaliya da suka shiga gasar a karon farko.
Bayan tankaɗe da rairaya an zaɓi 30, sannan aka sake rairayewa aka zaɓi 12, daga ciki kuma aka sake zaɓar biyar da suka fi yi zarra.
Biyar ɗin farko sun haɗa da Denmark da Nijeriya da Mexico da Thailand da kuma Venezuela.
