Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
A yayin da ake ci gaba da fuskantar taɓarɓarewar hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar nan, sama da jihohi 15 na Arewan Nijeriya sun kashe kimanin kuɗi Naira Biliyan 45 kan shirye-shiryen rage raɗaɗin talauci a cikin watanni shida na farkon shekarar 2024, kamar yadda wani bincike ya nuna.
A ranar Juma’a, Hukumar ƙididdiga ta ƙasa ta bayyana cewa hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya haura zuwa kashi 33.88 a watan Oktoban 2024, daga kashi 32.70 a watan Satumba.
A watan Janairu, hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar ya kai kashi 29.90 cikin 100, lamarin da ya nuna ya ƙaru da kashi 13 cikin 100 a cikin watanni 10 na farkon shekara.
Ana ganin tasirin hakan a galibin jihohin arewacin ƙasar, yankin da aka ce ya fi kowacce yanki talauci.
A watan Afrilun 2024, mai ba Shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya koka kan yadda talauci ya yi yawa a Arewacin Nijeriya, musamman Arewa maso Yamma.
A cewarsa, yankin ya kasance mafi yawan talauci a ƙasar, inda ya kai kashi 40.1 cikin 100 a shekarar 2019.
Da yake gabatar da takarda mai taken “Magance ƙalubalen rashin tsaro a Arewacin Nijeriya,” a wajen haɗakar lacca na Jami’ar Usmanu ɗanfodiyo Sokoto, Ribadu ya bayyana cewa Sokoto ce ta fi fama da matsalar tsaro a yankin.
Binciken da hukumar NBS ta ƙaddamar a jihohi 35 da babban birnin tarayya a shekarar 2022 ya kuma tabbatar da ƙaruwar talauci a Arewacin Nijeriya.
Binciken ya nuna cewa kashi 65 cikin 100 (mutane miliyan 86) na kashi 63 cikin 100 (mutane miliyan 133) talakawa a Nijeriya suna zaune a Arewa ne.
Ya bayyana cewa kashi 91 cikin 100 na al’ummar jihar Sokoto talakawa ne yayin da aka lissafta kason matalauta da dama ga sauran jihohin arewa kamar Jigawa (83.3), Zamfara (82.70), Yobe (81.70), Bauchi (81.30), Kebbi (79.10). Katsina (77.50), Gombe (77.40), Kano (68.80), Taraba (65.10), Borno (64.0), Neja (61.60), da Adamawa (59.90).
Wani bincike da aka gudanar ya nuna cewa kimanin jihohi 15 daga cikin 19 na Arewa sun kashe kuɗi N45,323,220,202 akan wasu shirye-shirye na rage raɗaɗin talauci a yankin tsakanin watan Janairu zuwa Yunin 2024.
Jihohin sun haɗa da Zamfara, Yobe, Filato, Neja, Nasarawa, Kwara, Kogi, Kebbi, Katsina, Kaduna, Jigawa, Gombe, Borno, Bauchi, da Adamawa.
