Nijeriya na iya samun tiriliyan N6.9 duk wata daga ɓangaren man fetur

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya na shirin samun kusan Naira Tiriliyan 6.99 a duk wata daga ɓangaren man fetur yayin da kamfanin mai na Nijeriya, NNPCL, tare da haɗin gwiwar masu ruwa da tsaki ya bunƙasa haƙo ɗanyen mai zuwa ganga miliyan 1.8 a kowace rana.

Matsakaicin farashin ɗanyen mai a shekarar 2024 ya kai dala 81 a kowace ganga. Wannan ya ɗan yi ƙasa kaɗan fiye da farashin 2022 na dala 101 a kowace ganga, amma ya daidaita idan aka kwatanta da farashin 2023 na dala 82 a kowace ganga.

Ta hanyar samar da 1.8mbpd kan farashin dala 81 kan kowace ganga, ƙasar za ta samu dala miliyan 145.8. A cikin kwanaki 30 wannan yana nufin dala biliyan 4.37.

A matsakaicin kasuwar canji ta gwamnati na N1,600 da dala 1, wannan yana ba da Naira Tiriliyan 6.99, wanda shi ne kiyasin adadin da Gwamnatin Tarayya za ta iya samu a kowane wata saboda hauhawar farashin mai.

Babban jami’in kamfanin mai na NNPC, Mele Kyari ne ya sanar da samun nasarar haƙo man fetur a yayin wani taro da aka yi na yaƙin samar da mai a hedikwatar NNPC a ranar Alhamis a Abuja.

Taron wanda Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur Heineken Lokpobiri ya jagoranta, ya samu halartar Shugaban Hukumar NNPC, Cif Pius Akinyelure; GCEO na kamfanin, Kyari; Babban jami’in kuɗi, Adedapo Segun; Mataimakin shugaban samar da man fetur, Isiyaku Abdullahi; Babban Jami’in Zuba Jari a ɓangaren man fetur na Kamfanin NNPC, Bala Wunti, da dai sauransu.

A zaman tattaunawa da kwamitin kuɗi na majalisar dattawa a majalisar dokokin ƙasar a watan Disambar shekarar da ta gabata, GCEO ya tabbatar da cewa hasashen da aka yi kan haƙo ɗanyen mai da ma’auni na farashin kasafin kuɗin shekarar 2024 gaskiya ne kuma mai yiwuwa.

Kamfanin ya kuma ce yanzu haka yana samar da iskar gas mai siffar ‘cubic’ biliyan 7.4 don samar da ababen more rayuwa na iskar gas, musamman AKK. Wannan ci gaba ne daga daidaitattun tsarin cubic biliyan 6.1 na iskar gas a farkon shekara.

Hukumar ta NNPCL ta bayyana cewa, nasarar da aka samu, wanda ya yi daidai da kasafin kuɗin gwamnati, ya nuna ƙwazon kamfanin da dukkan ƙungiyoyin ta a makonnin da suka gabata.

By ukarofi