Daga RABIU SANUSI a Kano
Al’ummar garin Ture Balam cikin masarautan Kaltungo sun amsa gayyatan Uban ƙasa Mai Kaltungo don noman ciyawa a gonan Uban ƙasa na al’umma da ke cikin garin Ture Balam.
Mai Kaltungo ya horar da al’ummar ne domin su riƙa noma daidai da zamani.
Haka zalika, duk lokacin da wani aiki ya tashi na wannan gonar al’ummar garin Ture Balam su suke gabatar da aikin tun kama daga dashen rogon, noma zuwa girbin rogon kuma gona ne da Uban ƙasar Kaltungo ya yi don ya taimaki jama’ar da ke ƙarƙashin ikon masarautarsa.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, waɗanda za su fi cin gajiyar wannan gona su ne al’ummar garin Ture Balam cikin masarautan Kaltungo.
Haka zalika, Uban ƙasa Injiniya Saleh Muhammad a shekara guda da ta gabata an gudanar da irin wannan ƙoƙari a garin Ture Okwaldi, inda al’umma suka amfana da roga.
Sannan kuma, sun koyi yadda ake dashen rogo na zamani tare da samun iri.
A wannan shekara, Uban ƙasa ya garzaya zuwa wani gari daga cikin masarautarsa, wato Ture Balam wanda idan Allah ya kai mu aka cire wannan rogon suma sun koyi yadda ake dashen rogo na zamani.
”A shekara mai zuwa kuma Uban ƙasa zai ƙara garzayawa zuwa wani ɓangare na Masarautar Kaltungo don cigaba da gabatar da wannan aikin alheri.
