Gwamnatin Tarayya na shirin tilastawa ma’iakatu da hukumomin gwamnati da cewa wajibi ne su amshi masu hidimar ƙasa da aka turo ma’aikatun su.
Ministan ci gaban matasa na ƙasa, Ayodele Olawande ya bayyana haka a wani taron manema labarai a Abuja. Ministan ya yi wannan martani a dalilin yawan ƙorafe-ƙorafe da suke samu yadda ma’aikatun gwamnati ke ƙin amsar masu yi wa ƙasa hidima, ya na mai tabbatar da cewa za su rubuta takarda su aika wa shugaban ƙasa.
Idan ba a mance ba, a cikin watan Nuwamba gwamnati ta dakatar da dokar da ke hana masu yi wa ƙasa hidima yin hidima ga kamfanoni masu zaman kansu. Yin hakan ya bada damar yin hidima ga wannan kamfanonin kamar su bankuna da sauran su.
Ministan ya tabbatar da cewa suna iya bakin ƙoƙarin su domin ganin ma’aikatun gwamnati sun bi wannan umarnin.
Daga ƙarshe ya ba da tabbacin cewa nan bada jimawa ba, masu yi wa ƙasa hidima za su fara amsar alawus na ₦77,000.
