MHWUN ta ƙasa ta naɗa Mannir Suleiman mamba na ƙwararru a ɓangaren kiwon lafiya

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Ƙungiyar malaman kiwon lafiya da unguwarzoma ta ƙasa ta tabbatar wa tsohon shugaban ƙungiyar a Jihar Katsina Mannir Suleiman da zama mamba a kwamitin ƙwararru a ɓangaren kiwon lafiya.

A wata wasiƙa ɗauke da sa hannun sakataren ƙungiyar na ƙasa Auwalu Yusuf kiyaye, ƙungiyar ta amince da haka ne a babban taron ta karo na 50 da ya gudana a babban zauren taro na ƙungiyar da ke Abuja.

Ƙungiyar tace ta ɗauki wannan shawara ne a bisa ƙwarewar sa da irin ayyuka da ya gudanar lokacin da ya ke riƙe da ƙungiyar a Jihar Katsina.

Wasiƙar ta bayyana yaƙinin ƙungiyar na amfani da ƙwarewar sa wajen ciyar da ƙungiyar gaba.

Haka gwamnatin Jihar Katsina ta bashi muƙamin mamba a hukumar gudanarwa a hukumar kula da kiwon lafiya a matakin farko a jihar.

Da yake tsokaci akan muƙaman da malam Mannir Suleiman ya samu, shugaban ƙungiyar a Jihar Katsina Malam Bashir Ibrahim Gyaza ya taya tsohon shugaban murna.

“Wannan muƙami da Suleiman ya samu, ya dace ƙwarai duba da irin cigaba da ya samar lokacin da yake shugaban ƙungiyar a Katsina”.Gyaza yace.

Ya yi fatan zai amfani da ƙwarewar sa da jajircewar sa wajen ciyar da ƙungiyar a matakin jiha da ƙasa baki ɗaya.

By ukarofi