
Daga AMINU ASID
Bugawar zuciya wadda a turance ake kiran t da ‘heart attack’, al’amari ne dake buƙatar taimakon gaggawa; kai tsaye yana faruwa ne sa’ilin da gudanar jini zuwa ga zuciyar ya katse; sakamakon toshewar hanyoyin jinin dake kai mata jini ko tsukewarsu.
Kamar sauran sashen jiki, zuciya ta dogara ne ga jini wajen samun sinadaran abinci, iska da sauran su. Saboda haka, katsewar gudanar jinin yana jawo rashin samun waɗancan muhimman abubuwa, wanda hakan ke jawo mutuwar sashen (ƙwayoyin halittar) zuciyar.
Zuciya dai muhimmiyar sashe ce ta jiki, wacce aikin ta ba dare ba rana shine tura jini (ta cikin hanyoyin jinin) zuwa ga sashe daban-daban na jiki kama daga huhu, ƙwaƙwalwa da sauran su. A ɗaya bangaren kuwa ita ma tana samun nata kason jinin ne ta bututun da ake kira ‘coronary arteries’.
Babban maƙasudin bugawar zuciyar kuwa shine toshewa ko tsukewar wancan bututu da ake kira ‘coronary arteries’.
ABUBUWAN DAKE JAWO ZUCIYA TA BUGA
Manyan dalilai biyu dake haddasa bugawar zuciya sune kamar haka:
- Toshewar hanyoyin jini dake bai wa zuciya jini wato ‘coronary arteries’:
Wannan yana faruwa ne sakamakon taruwar kitse a cikin su hanyoyin. Hakan kuma yana jawo tare jinin har ta kai ga ya taru sannan kuma ya dunƙule; a ƙarshe kuma ya toshe su hanyoyin. - Tsukewar ko ƙandarewar su hanyoyin jinin na zuciya: Wannan yana faruwa ne dalilin shan taba, amfani da miyagun ƙwayoyi (na shaye-shaye) kamar ‘cocaine’.
ALAMOMIN BUGAWAR ZUCIYA
Alamomin na iya bambanta tsakanin maza da mata, wasu suna iya ƙin samun alamomin ma. Alamomin sun ƙunshi
- Ciwon ƙirji mai kama da tsukewar ƙirji, da yake bazuwa har ga wuya, haɓa, da baya.
- Tashin zuciya, ciwon ciki
- Ɗaukewar numfashi
- Gumi mai sanyi
- Jiri
- da sauran su
ABUBUWAN DAKE TASIRI GA FARUWAR BUGAWAR ZUCIYA
Waɗannan abubuwa da yawan su ana iya canja su (domin kare kai). Sun haɗa da:
- Shan taba
- Hauhawan ƙarfin gudun jini (BP) haɗe da wasu larurorin kamar ciwon suga, nauyi sama da ƙima
- Shekaru: 45 zuwa sama (ga maza), 55 zuwa sama (ga mata).
- Yawaitar kitse: Musamman samfurin da akewa laƙabi da ‘bad cholesterol’/LDL
- Nauyi sama da ƙima
- Faruwarta a dangi na kusa; kamar uwa ko uba, ƴan uwa
- Rashin motsa jiki
- Amfani da miyagun ƙwayoyi: kamar cocaine, amphetamines
- Samun jijjiga yayin haihuwa (preeclampsia)
- Wasu larurorin kamar ciwon gaɓoɓi (R.A).
ILLOLIN BUGAWAR ZUCIYA
- Yana jawo hargitsewar bugun zuciya; wanda yana iya sabbaba shanyewar ɓarin jiki da sauran illoli
- Yana iya jawo gazawar zuciya, sakamakon mutuwar sashe nata mai yawa
- Yana iya jawo mutuwar farat ɗaya.
SHAWARWARI A TAƘAICE
Abin sani ga kowa da kowa shine; wannan larura ce mai buƙatar agajin gaggawa, dole ne suk sanda aka fahimce ta, to ayi gaggawar kai mutum zuwa asibiti ko a kira taimakon gaggawa. Sannan:
- A bar shan taba ko shaƙar hayaƙinta daga wani.
- A rinƙa motsa jiki a yawancin ranakun sati na tsawon mintuna talatin
- A nesanci jibgewa guri guda, wato dai ɗabi’ar rashin son motsa jiki
- Ayi hattara da cin kitse, a riƙi lafiyayyen abinci mai ƙunshe da muhimman nau’o’in abinci.
- A nesanci shaye-shaye
- A riƙa zuwa asibiti ko Pharmacy na kusa domin gwajin karfin gudun jini (BP) dama samun shawarwari akan kiwon lafiya
- A nesanci shan magunguna ba tare da izini ko saɓanin shawarwarin ƙwararru ba.
