
Daga BELLO A. BABAJI
Mambobin ƙungiyar matasan Arewa ta AYPAS sun yi jimamin rasuwar tsohon soja mai ritaya, Sajan Garba Gambo.
Matasan sun bayyana mutuwar tsohon sojan a matsayin babban rashi ga Nijeriya.
Sakataren ƙungiyar, Kwamared Salihu Ɗantata Mahmud ya faɗi hakan a Abuja a lokacin da ya ke magana game da mutuwar jarumin sojan, ya na mai cewa ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa rundunar sojin Nijeriya hidima.
Ya yi aiki a kwalejin sojoji dake Zaria da Bataliyar sojoji ta Janguza a Kano da kuma sansanin sojoji dake yankin Bakassi.
Ya ƙara da cewa suna miƙa ta’aziyarsu ga rundunar sojoji da iyalansa da abokan aiki da kuma abokanan arziƙi.
Sun kuma yi addu’ar a gare shi na fatan samun rahamar Allah (SWT).
Mamacin ya rasu ya bar mata ɗaya da ƴaƴa da kuma jikoki. Ƴaƴan sun haɗa da Mustapha, Zainab, Ibrahim, Maryam, Rabi da A’isha. Sai kuma jikansa mai suna Salihu Mahmud Salihu na tsangayar nazarin Harkokin Ƙasa da ƙasa (International Relations) a Jami’ar North West, Kano.
