

Daga UMAR AƘILU MAJERI a Dutse
Kimanin ɗalibai 324 ne suka fafata a gasar musabaƙar karatun Al-ƙur’ani ta bana da aka gudanar a Jihar Jigawa.
A yayin gasar, an fitar da gwarzayen shekara a ɓangaren maza da mata inda Gwamna Namadi ya bai wa gwarzo da gwarzuwa kyautar N700,000.
Malam Abduljabar Idris Gwaram shi ne ya zama gwarzon shekara da maki 89.8, yayin da Habibu Abdullahi Kiyawa ya zo na biyu da maki 80, sai kuma Auwal Abdullahi Miga ya samu maki 73.8 a ɓangaren maza kuma a hadda da tafsiri da lugga.
A ɓangaren mata kuwa, Zainab Abdullahi Dutse ce ta zama gwarzuwar shekarar da maki 81.2, sai kuma Zainab Abdullahi Haɗejia ta rufa mata baya da maki 67.7.
Sai kuma Aisha Ahmed Gagarawa wacce ta zo ta uku da maki 65 inda dukkansu Kakakin Majalissar dokokin jihar Alh. Haruna Aliyu Ɗan Gyatin ya ba su kyautar kuɗaɗe.
Ya bai wa waɗanda suka zo na ɗaya a ɓangarorin biyu kyautar N100,000 ga kowannen su, sai waɗanda suka yi na biyu da na uku da kowannen su ya samu N50,000.
Waɗanda suka yi na huɗu zuwa mataki na biyar kuwa, sun samu Naira dubu talatin-talatin.
Yayin da suma sauran ɗaliban da suka shiga gasar a ya ba su kyautar dubu goma-goma.
Da ya ke jawabi Gwamnan jihar, Malam Umar Namadi ya ce ana samun ci-gaba sosai a ɓangaren gasar karatun Al-ƙur’ani Mai tsarki a kowacce shekara a jihar.
Ya yi godiya ga Allah SWT bisa ni’imar da Ya yi wa jihar ta makaranta da hafizan Al-ƙur’ani inda ya ce hakan ba ƙaramar nasara ba ce da Allah Ya yi wa jigawa.
Namadi ya kuma yaba wa Malaman da suka bayar da gudunmawarsu wajen shirya masaɓakar kuma suka tsaya wajen karantar da ɗaliban tare da ba su horo da sanya ido wajen ganin an samu nasara a gasar.
Ya ƙara da cewar gwamnati za ta bai wa lamarin duk kulawar da ake buƙata saboda haka ya hori matasa su tsunduma wajen Shiga gasar musabaƙa a duk inda suke a jihar.
Shugaban Hukumar da ta shirya musabaƙar, Malam Mubarak Hassan wanda shi ne sakataren Hukumar shirya Musabaƙa ta jihar ya yaba wa gwamnatin jihar bisa irin gudun mawar da ta bayar wajen ganin an samu nasara a gasar ta bana.
