



Daga BELLO A. BABAJI
Kimanin ƴan Najeriya 45,689 ne suke jarrabawar sharar fage ta neman aiki a Babban Kamfanin Man fetur na Ƙasa, NNPCL.
Jarabawar wadda ake yin ta a bayyane don bai wa kowane ɗan ƙasa damar samun aikin yi, na daga cikin manufofin gwamnatin Shugaba Tinubu na ganin an daina mayar da talakawan ƙasar saniyar-ware a ɓangaren samun aiki a manya da ƙananan ma’aikatun ƙasar.
Cikin marubuta jarrabawar har da masu buƙata ta musamman da aka tanadar musu da waje na musamman inda suka duƙufa akan na’urorin da aka tanada a cibiyoyin NNPCL dake sassa daban-daban na faɗin ƙasar nan.
Masu sa-ido akan sahihancin jarabawar sun haɗa da shugaban gudanarwar kamfanin Malam Mele Kyari wanda a safiyar yau ya ziyarci cibiyar samar da albarkatu ta Ansar-Ud-Deen Society Centenary Resource Center da ke Maitama a Abuja, don tabbatar da ana bin duka tsare-tsaren da aka shimfida don tabbatar da gaskiya da riƙon amana.
Kyari ya jaddada cewa ma’aikatar na shirye da ɗaukan waɗanda suka cancanta aiki, kuma za su fito ne daga cikin mutane 45,689 dake neman gurbin aikin a faɗin ƙasar.
